Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 30 A Jihar Borno


Kwalejin Horar Da Jami'an Soji - NDA, Kaduna
Kwalejin Horar Da Jami'an Soji - NDA, Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta sami nasarar halaka sama da ‘yan ta’adda 30 bayan wani samame da dakarun hadin gwiwa wato OPHK suka kai a wata maboyan ‘yan ta’addar a jihar Borno da ke yankin arewa maso Gabas.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce farmakin wani bangare ne na kara kaimi da sojoji ke yi a yankin don kawo karshen matsalolin tsaro a yankin Arewa maso gabas da sauran sassan kasar da dama.

Da sanyin safiyar ranar Asabar 30 ga watan Oktoban da ta gabata ne yan kungiyar sa kai suka lura da zirga-zirgar wasu manyan motocin yaki masu bindigogi guda shida a cikin dajin Sambisa, wadanda daga bisani suka kasance a wani kauye kusa da garin Yuwe, in ji Janar Nwachukwu.

Nwachukwu ya ce "baya hakan ne manyan motocin masu dauke da bindigogin suka koma wani wuri mai nisa, inda wasu ’yan ta’adda suka hadu da sauran wadanda suka tuko motocin, a wani abu mai kama da taron mayakan."

Rahotanni sun yi nuni da cewa sama da mayakan Boko Haram da na ISWAP 50 ne aka hango sun tattaru a wurin taron kuma bayan gano maboyar ‘yan ta’addan nan take sashin mayakan sama na dakarun hadin gwiwa na OPHK ta aike da jiragen sama guda biyu domin gudanar da bincike kan wurin aka kuma dauki matakan da suka dace, kamar yadda janar Nwachukwu ya bayyana.

Nwachukwu ya kara da cewa harin sama da aka kai a cikin duhu kan maboyar mayakan ya sami nasara inda wasu majiyoyi na cikin garin suka tabbatar da cewa ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP sama da 37 sun mutu kuma wasu da dama daga cikinsu sun samu raunuka daban-daban kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Haka kuma, Nwachukwu ya kara da cewa, baya ga kamala aikin luguden wuta ta sama da jirgin yakin sojin sama ya yi kuma ya koma matsuguni, jami’an dakarun hadin gwiwar sojin saman sun gano wasu motocin kira mai bindigogi guda hudu kimanin kilomita shida da kudu maso yammacin garin Bama.

A cewar mai magana da yawun rundunar sojin, nasarar hadin gwiwa da dakarun sama da na kasa na rundunar soji suka gudanar tare da samun goyon bayan sauran jami’an tsaro a karkashin Operation Hadin Kai, ya sake jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen yakar ta’addanci da ‘yan tada kayar baya a kasar.

Kazalika Janar Nwachukwu ya ce dakarun na OPHK sun ci gaba da jajircewa a kokarinsu na kawo karshen mayakan Boko Haram da sauran miyagun iri da ke haddasa matsalar rashin tsaro a kasar.

XS
SM
MD
LG