Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Yi Zanga-Zanga Kan Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Filato


Tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Filato, Abok Nuhu Ayuba.
Tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Filato, Abok Nuhu Ayuba.

Matasa a jihar filato sun yi tattaki zuwa majalisar dokokin jihar Filato domin nuna bacın ransu kan tsige matashi dan uwansu wato kakakin majalisar, Abok Ayuba Nuhu da 'yan majalisar suka yi.

Gomman matasan da ke zanga-zangar sun fantsama kan titunan birni Jos ne tun da misalin karfe 4 na sanyin asubahin yau Litinin, har suka kai harabar majalisar dokokin jihar.

Fusatattun matasan sun ce ba su yarda da yanayin da majalisar dokokin ta tsige Abok Ayuba Nuhu a makon jiya ba.

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai majalisar dokokin jihar ta Filato ta yi wani zama, inda ta bayyana tsige shugaban na ta Abok Nuhu, tare da maye gurbinsa da Sanda Yakubu, daga mazabar Pingana ta karamar hukumar Bassa.

Rahotanni daga jihar Filaton sun bayyana cewa 'yan majalisar 16 ne daga cikin 24 suka jefa kuri’ar amincewa da tsige Abok Nuhu, a zaman majalisar na ranar Alhamis, wanda mataimakin kakakin majalisar Saleh Yipmong ya jagoranta.

Wasu majiyoyi kuma na cewa tsige Nuhu baya rasa nasaba da rashin jituwa da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Simon Lalong, sakamakon yadda shi Nuhu ke fitowa fili yana sukar gwamnan bayan harin da aka kai a unguwar Yelwan Zagam da ke yankin Jos ta Arewa, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya ta yi nuni da cewa shugaban majalisar ya yi ta caccakar gwamna Lalong a bainar jama’a tun bayan harin na unguwar Yelwan Zagam, haka kuma ya daina halartar ayyukan gwamnati a jihar.

Har kawo yanzu dai ba bu cikakken bayani kan wani laifi ko dalilin tsige kakakin majalisar dokokin ta jihar Filato.

XS
SM
MD
LG