Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Sudan Sun Rusa Majalisar Mulkin Kasar Bayan Tsare Firai Minista Abdalla Hamdok


Abdalla Hamdok
Abdalla Hamdok

Hamdok, masanin tattalin arziki ne da ya taba aiki da Majalisar Dinkin Duniya. An zabe shi a matsayin Firai minista na wucin gadi a watan Agustan 2019.

Babban Janar din sojin kasar Sudan Janar Abdel Fattah Al Burhan, ya ayyana dokar ta-baci tare da rusa majalisar mulkin kasar da ke kunshe da sojoji da fararen hula da ta kwashe shekara biyu tana mulki.

Al Buran ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a yau Litinin bayan da dakarun kasar suka tsare Firai Minista Abdalla Hamdok da wasu jami’an gwamnatin kasar.

Ma’aikatar yada labaran kasar wacce ke ci gaba da fitar da sanarwa, ta ruwaito cewa an tsare Hamdok ne bayan da ya ki nuna goyon bayan ga juyin mulkin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa da sanyin safiyar Litinin wasu sojojin kasar suka fada gidan Firai Ministan suka tsare shi.

Daga cikin wadanda ake tsare da su a gidan Hamdok har da ministocinsa hudu da wani farar hula daya, wanda mamba ne majalisar zartarwa a cewar gidan talabijin na Al-Hadath.

Rahotanni har ila yau sun ce an tsare da dama daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar da ke mulki da wasu jami’an gwamnati sannan an katse hanyoyin sadarwar intanet a Khartoum, babban birnin kasar ta Sudan, kamar yadda wasu ‘yan jarida da masu fafutuka suka tabbatar.

Baya ga haka, an kuma rufe filin tashin jirage na kasa da kasa da ke birnin.

Masu zanga-zangar kin jinin mulkin soji a Sudan
Masu zanga-zangar kin jinin mulkin soji a Sudan

Ma’aikatar yada labaran kasar ta Sudan yi watsi da juyin mulkin tare da yin kira da a saki dukkan wadanda ake tsare da su.

Hamdok, masanin tattalin arziki ne da ya taba aiki da Majalisar Dinkin Duniya. An zabe shi a matsayin Firai minista na wucin gadi a watan Agustan 2019.

Shi ne yake jagorantar gwamnatin rikon kwaryar kasar bayan da aka hambarar da tare da tsare tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir mai mulkin kama karya.

Wani mai zanga-zanga a Sudan
Wani mai zanga-zanga a Sudan

Kasar ta Sudan na shirin yin zabe a karshen shekarar 2022, zaben da aka haramtawa Hamdok tsayawa takara.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da wani bangare na kasar Sudan ta yi kira da a mika mulki ga farar hula ya yi gargadin cewa akwai yiyuwar juyin mulki, a yayin wani taron manema labarai da wasu gungun mutane da ba a san ko su waye ba suka nemi hana tun farko.

Kasar Sudan dai na ta fuskantar sauye-sauye mai cike da rudani da rarrabuwar kawuna tsakanin bangarorin siyasa da gwagwarmayar samun madafun iko tun bayan hambarar da shugaba Bashir na watan Afrilun shekarar 2019.

A makon da ya gabata, dubban masu zanga-zanga suka bazama kan titunan kasar suka nuna adawarsu da dawowar sojoji kan karagar mulki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG