Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Kammala Zaben Gwamnan Jihar Anambra A Ranar Talata -INEC


Zauren da ake tattara sakamakon zaben jihar Anambra (Hoto: Channels TV)
Zauren da ake tattara sakamakon zaben jihar Anambra (Hoto: Channels TV)

Hukumar zabe ta Najeriya mai zaman kanta wato INEC ta dakatar da aikin tattara sakamakon zaben jihar Anambra da aka fara gudanarwa a ranar asabar inda ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin jawabin jami’ar tattara sakamakon zaben, Farfesa Florence Obi, wacce nauyin sanar da sakamakon zaben ya rataya a wuyanta.

Da sanyin safiyar yau Litinin ne Farfesa Florence ta bayyana cewa "zaben na jihar Anambra bai kammala ba," a hedkwatar hukumar da ke babban birnin jihar wato Awka.

Kazalika Florence ta alakanta dalilin da ya sa zaben bai kammala ba da yadda masu kada kuri’a ba su sami damar jefa krui’unsu ba a karamar hukumar Ihiala ta Jihar ta Anambra.

Florence ta kara da cewa za’a sake gudanar da zaben karamar hukumar Ihiala a ranar talata a bisa tanadin dokar zabe ta Najeriya.

Kafin dakatar da aikin tattaro sakamakon zaben, dan takarar jam’iyyar APGA, kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Farfesa Charles Soludo ne ke kan gaba da mafi yawan kuri’u na dubu 103,946 a zaben da aka gudanarwa a kananan hukumomin mulki 20, daga cikin 21 na jihar.

Sauran ‘yan takara kamar su Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP ya zo a matsayin na mai yawan kuri’u na biyu da kuri’a dubu 51,322, sai Andy Uba na jam’iyyar APC ya zo na uku da kuri’a dubu 42,942.

Rahotanni daga jihar dai sun yi nuni da cewa adadin mutanen da suka yi rajista don kada kuri’a sun kai dubu 246,638, inda hukumar INEC ta tantance mutane dubu 241,90.

Farfesa Florence dai dake zaman jami’ar hukumar INEC, ta bayyana cewa a halin yanzu yawan kuri’un da aka kidaya sun kai dubu 229,521, baya ga kuri’u dubu 7,841 da suka lalace kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kafin fara gudanar da zaben na ranar Asabar dai, wasu fayafan bidiyo sun yi ta yaduwa a kafaffen sada zumunta na zamani inda aka yi taho-mu-gama da dan takarar jam’iyyar APGA farfesa Charles Soludo da na jam’iyyar APC Uba wanda ke ikrarin cewa shi ya mika sunan Soludo ga yayan shi a ka nada shi gwamnan babban bankin Najeriya.

A wani faifan kuma an ga wani mutum mai sanye da rigar wata jam’iyya yana raba naira dari bi-biyu da lemon gwangwani ga wasu mutane a wani gini da ba’a tangence ba.

XS
SM
MD
LG