Babbar kotun tarayya a birnin Abuja ta ki amincewa da bukatar da lauyoyin Nnamdi Kanu suka gabatar na maida shi gidan gyara hali dake yankin Kuje a Abuja.
A yayin da ake ci gaba da kiki-kaka kan badakalar takardun Pandora da suka fito da bayanan wasu jiga-jigai a duniya, hade da wasu 'yan Najeriya a ciki da ake zargi da boye bayanan kadarori da suka mallaka ta kasuwanci a gabar teku.
Rahotanni daga jihar Nasarawa sun yi nuni da cewa maharan da ake zargin 'yan bindiga ne da suka sace mutane 4 a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Mararrabar Akunza sun tuntubi iyalansu tare da neman naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN kuma dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, Kingsley Moghalu, ya alakanta yawan barin kasar da matasa ke yi a halin yanzu ga matsin tattalin arziki da rashin kyawun yanayin rayuwa.
Wasu mahara da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kan kasuwar kauye a Goronyo da ke karamar hukumar Goronyo a gundumar mazabar gabashin jihar Sakkwato.
Mai taimakwa shugaban Najeriya Muhamaddu Buhari kan sha’anin yadda Labarai, Femi Adeshina, ya bayyana cewa a tarihin kasar bai ga wani dan siyasa da ya kai mai gidansa shugaba Buhari farin jini a wurin jama’ar kasa daga yankuna daban-daban ba.
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira ga jihohi da su sake nazari mai zurfi, su kuma yi Tunani kamar kasashe masu 'yancin cin gashin kai, ta yadda za su bunkasa samun kudaden shiga na cikin gida domin tafiyar da lamurransu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta 'yan yankin Naija-Delta, ta yi barazanar cewa dole ne yankin Arewa da yanzu haka ke mulkin kasar, ya jira har zuwa shekarar 2031, wato bayan shekaru 10 kenan, kafin ya sake samar da wani shugaban kasa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta soma gudanar da taron bitar ayyukan ministocinta na tsakiyar wa’adin mulki na biyu a birnin taraya Abuja.
Babban lauya a Najeriya kuma mai mukamin SAN, Femi Falana, ya nemi ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar kasar, Abubakar Malami, da ya karbo bashin dala biliyan 62 da kamfanonin man fetur na duniya 6 ke bin kasar a cikin wata wasika.
Wasu mazauna jihar Zamfara da suka kunshi kabilu daban-daban sun hada kai guri daya suka gudanar da addu’ar neman dauki kan matsalar tsaro da ke kara kamari a jihar.
Rundunar hadin gwiwar ‘yan sanda da 'yan sa kai a dajin Tsibiri da ke jihar Zamfara sun mika mutanen da suka ceto daga hannun 'yan bindiga ga gwamnatin jihar a aikin ci gaba da aiwatar da sabbin matakan yaki da batagari a jihar.
Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar mazabar jihar Bauchi ta Arewa ya bayyana cewa ba bu wani banbanci tsakanin 'yan fashin daji da' yan ta’adda domin duk suna aiki ne iri daya.
Hukumar kula da ’yan gudun hijira da wadanda yaki ya daidaita ta Najeriya ta bayyana cewa kimanin ’yan gudun hijirar Najeriya dubu 500 ne ka samun mafaka a kasashen waje.
Baya ga gurgunta harkokin yau da kullum a jihar, mayakan kungiyar Boko Haram na tilastawa mazauna karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da su aurar da ‘ya’yansu mata masu shekaru 12 da haihuwa.
Kasa da sa’o’i 24 da bayyana matsayarsu a game da tsarin mulkin karba-karba da maida shugabancin Najeriya kudancin kasar, masana shari’a da masu sharhi kan lamurran siyasa da ma wasu 'yan kasar sun ce hadin kan bangarori da bin kundin tsarin mulkin kasar shi ne mafita.
Mazauna garin Babban Gida dake karamar hukumar Tarmuwa na jihar Yobe sun yi ta tserewa daga gidajen su sakamakon harin mayakan Boko Haram.
Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar 4 ga Oktoban shekarar nan ta 2021 a matsayin ranar da za ta sake bude makarantu gwamnati da na masu zaman kan su.
Yan bindigar da suka sace yaran makarantar Bethel Baptist da ke Damishi a jihar Kaduna sun sake sakin karin wasu dalibai 10 daga cikin 21 da ke tsare a hannunsu, bayan shafe kwanaki 81 da aka yi garkuwa da su.
Mai taimakawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan harkokin yada Labarai, Femi Adesina, ya ce yadda shugaban ya karbi bakuncin Femi Fani-Kayode bayan sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya nuna yadda Buhari ke karrama mutane ko da masu zaginsa ne.
Domin Kari