Malami ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudana a ma’aikatar shari’a dake birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a inda ya ce kiran da Kanu ya yi ga magoya bayansa ya haddasa asarar rayuka da dukoyi.
Nnamdi Kanu ya kuma yi amfani da zanga-zangar Endsars da ta rikide zuwa tarzoma wajen ingiza mutane har aka rasa dimbin rayuka da dukiyoyi, in ji shi.
Kazalika, Malami ya ce a tsakanin jami’an tsaro an sami asarar rayuka mutane 175 da suka hada da ‘yan sanda 128, sojoji 37, sauran ma’aikatan tsaro 10 sakamakon harzuka magoya bayansa da Nnamdi Kanu ya yi aka yi mu su kisan gilla.
Baya ga jami’an tsaro da suka rasa ransu da aikin harzuka magoya bayansa da Nnamdi Kanu ya yi kuma sanadiyyar mutuwar wasu mutane da dama.
Daga cikin su akwai basarake Obi Nwanyi na al’umman Okudo, basarake Eze E. Anyaochukwu, Basarake Eze Samson Osonuwa na al’umman Ehiebene na Owerri, Chike Akunyili, mijin marigayiya tsohuwar babbar darakatar hukumar NAFDAC Dora Akunyili da dai sauransu da ya yi sandiyar mutuwarsu.
A ranar Alhamis Kanu ya sake bayyana a gaban kotun tarayya da ke Abuja a ci gaba da sauraren shari'ar da ake masa inda ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.
A latsa wannan sauti don jin cikakken jawabin ministan shari’a Abubakar Malami.