Masu ruwa da tsaki daga bangarori dabam-daban a Najeriya ciki har da ma’aikatar ilimi, hukumar kidayar al’uma, da ofishin babban bankin duniya a kasar sun ce ya kamata duk masu hannu da shuni su bada gudummowa ga ilimin yara mata ta yadda za a fi bada fifiko a kai don habbaka tattalin arzikin kasar.
Masana kimiyya da fasaha sun jaddada mahimmancin rawar da 'yan jarida za su taka wajen fahimtar da al’umma kan alfanun kayan abinci ‘yan aure a yaki da yunwa da fari a nahiyar Africa da ma duniya baki daya.
Kotun kolin ma’aikata ta Najeriya ta ba kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU umurnin dakatar da yajin aiki, a daidai lokacin da kungiyar daliban kasar ta NANS ta ke kan zanga-zangar datse titin zuwa filin jiragen sama a Legas, kuma zata yi a Abuja saboda yajin aikin malaman.
Tawagar aiki na neman samar da cigaban al’umma ta Core Working Group karkashin gwamnatin tarayyar kasar ta yi kira ga ‘yan jaridu da su hada gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki baya ga gwamnati don cimma manufofin ci gaban al’umma a Najeriya.
A yayin da ake ci gaba da nuna alhini kan mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta II a fadin duniya, ba a bar Najeriya a baya ba inda wasu jiga-jigai a kasar suka yi ta bayyana irin yadda suke jimamin mutuwarta, tare da ambata irin tasiri da marigayiyar take da shi a duk duniya.
Dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa sanata Kashim Shattima sun sha alwashin bai wa mata sama da kaso 35 cikin 100 na damarmaki da mukamai idan har suka sami nasara a zaben shekarar 2023.
Masu rike da sarautun gargajiya a arewacin Najeriya sun kudiri aniyar ganin karfafawa mata gwiwa don ganin an dama da su a harkar siyasar kasar, tare da kawo karshen barazanar da ake musu wanda ke hana su taka rawar gani a fannin musamman ma a zaben shekarar 2023 mai gabatowa.
A yayin taron, an ba da muhimmanci ga tunatar da gwamnati a kan gibin da ake samu wajen kasafta kudi ga bangarorin ilimi, kiwon lafiya da ma inganta sana’o’in al’umma.
Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Najeriya wato FRSC ta bayyana cewa karuwar hadurra da ake gani na da alaka da tu’amalli da ababen maye a bangaren direbobi musamman a kwanakin karshen mako.
Kamfanin jiragen saman jigilan fasinjoji na Emirate yace zai dakatar da aikin jigilan fasinjoji zuwa Najeriya daga ranar 1 ga watan Satumba sakamakon matsalar kin bai wa kamfanin damar daukar kudadensa da ya sayar da tikiti a kasar .
Biyo bayan kiran da ma’aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya ta yi wa hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa akan ta fara kamen masu yin buga fasfo ta bayan fagge, hukumar ta EFCC ta shawarci ma'aikatar da ta bullo da hanyoyin magance matsalar da kan ta.
Hukumar EFCC ta yi karin haske kan rashin cimma matsaya tsakanin bangaren hukumar da dakataccen babban akanta janar na tarayyar Najeriya a game da bukatar neman sassauci a maida kudadden da ake zargin ya wawure ga lalitar gwamnat don a rage tsaurin hukuncin kotu da ake kira "plea bargain."
Wasu masu neman takarar kujerar gwamna a jihohin Najeriya na ci gaba da yin alkawura idan jama'a suka ba su dama a zaben 2023.
Wani rahoton binciken masana ya nuna cewa a kowacce rana 'yan ta'adda na kashe akalla mutane 37 a sassan Najeriya dabam-daban, al'amarin da masana tsaro ke ganin ya kamata gwamnati ta sauya salo a yaki da 'yan ta'adda a kasar.
Domin Kari