Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bada Muhummanci Ga Ilimin Yara Mata Zai Taimaka Wajen Habbaka Tattalin Arziki - Masana


Mahalarta taron bunkasa ilimi
Mahalarta taron bunkasa ilimi

Masu ruwa da tsaki daga bangarori dabam-daban a Najeriya ciki har da ma’aikatar ilimi, hukumar kidayar al’uma, da ofishin babban bankin duniya a kasar sun ce ya kamata duk masu hannu da shuni su bada gudummowa ga ilimin yara mata ta yadda za a fi bada fifiko a kai don habbaka tattalin arzikin kasar.

ABUJA, NIGERIA - Masu ruwa da tsakin dai sun bayyana hakan ne a yayin wani taron bita da hukumar kidayar al’uma tare da hadin gwiwar ofishin babban bankin duniya a Najeriya suka shirya don karfafa wa ‘yan jarida gwiwa a kan ci gaba da yada labaran da zasu farkar da gwamnati, da masu hannu da shuni, da kuma dukkan al’uma a game da alfanun bai wa yara musamman mata ilimi don bunkasa tattalin arzikin kasar.

Masanan sun bayyana cewa bai wa yara mata ilimi tamkar ilimantar da dukkan al’uma ne.

Malama Amina Buba Haruna, jagorar shirin bai wa yara mata ilimi da tallafi wato AGILE, ta bayyana cewa rashin fahimtar yadda sha’anin ilimi yake shi ne babban kalubalen da ake fuskanta.

Amina Buba Haruna
Amina Buba Haruna

Kusan kullum masu ruwa da tsaki na kokawa a game da rashin bada muhimmanci ga bangaren ilimi a kasafin kudin shekara-shekara na Najeriya, ko a ‘yan watannin da suka gabata sai da Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya ce ya kamata kasafin kudin bangaren ilimi a kasar na shekarar 2022 ya kasance Naira tiriliyan 1 da biliyan 140, kwatankwacin kaso 8 da digo 4 a maimako kaso 5 da digo 4 da aka ware.

Honarabul Muhammad Usman, mamba ne a kwamitin inganta ayyuka na babban bankin duniya wato Enhanced Team a turance, ya bayyana cewa babu abinda ya fi ilimi amfani a duniya la’akari da cewa ko a musulunci an bada muhimmanci ga neman ilimi.

Muhammad Usman
Muhammad Usman

Yanayin tsaro da ake ciki a Najeriya na daga cikin abinda ke hana dubban yara zuwa makaranta, in ji malama Balaraba Muhammad, ma’aikaciya a sashen ilimin jami’a a ma’aikatar ilimi ta kasa.

Kwararriya a fannin ilimi kuma ma’aikaciya a ofishin babban bankin duniya a Najeriya, wacce kuma jagora ce mai kula da shirin bai wa yara mata ilimi da tallafi wato AGILE, Aisha Garba, tace idan ‘ya’ya mata suka sami ilimi zasu taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa kuma ya kamata gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su bada muhimmanci ga ilimin yara mata mafi karanci na sakandare.

Aisha Garba
Aisha Garba

Alkaluman kididdiga dai sun yi nuni da cewa a shekarar 2022, an kasfta ba ma’aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya Naira biliyan 65 da miliyan 300, hukumar ilimi ta bai daya wato UBEC mai kula da harkokin ilimi a matakin firamare da sakandare ta samu Naira biliyan 77 da miliyan 600.

An kuma raba ragowar Naira biliyan 599 da miliyan 600 a cibiyoyi da hukumomi 21 da ke karkashin ma’aikatar ilimi ta tarayya, inda kowacce cibiya ta sami naira biliyan 28 da miliyan 500.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG