Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Na Juyayin Mutuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta II


Waiwaye Kan Rayuwar Sarauniyar Elizabeth Ta Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00

Waiwaye Kan Rayuwar Sarauniyar Elizabeth Ta Biyu

A yayin da ake ci gaba da nuna alhini kan mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta II a fadin duniya, ba a bar Najeriya a baya ba inda wasu jiga-jigai a kasar suka yi ta  bayyana irin yadda suke jimamin mutuwarta, tare da ambata irin tasiri da marigayiyar take da shi a duk duniya.

ABUJA, NIGERIA - Batun mutuwar ta Sarauniya Elizabeth tabbas wani babban lamari ne da ya girgiza duniya, kuma ya sa mutane ke sharhi daban-daban da tofa albarkacin bakinsu kan rashin sarauniyar, wacce da dama ke daukarta a matsayin uwa ga duka jama'ar duniya, lamarin dake nuna wani irin gaggarumin dattako.

A cewar fitacciyar ‘yar siyasa kuma tsohuwar kwamishinayar noma ta Jihar Kano, Dakta Baraka, tsarin shugabancin da Elizabeth ta yi a lokacin rayuwarta ya nuna shugabanci na gari da kaunar zaman lafiya.

Shi ma Ambasada Dauda Danladi wani tsohon ma'aikacin gwamnati a matakai daban-daban sannan tsohon jakadan Najeriya a kasar Pakistan, ya bayyana irin yadda yake kallon tsarin shugabancin marigayiya Elizabeth da rashinta zau kawo.

Sarauniyar Inglia
Sarauniyar Inglia

A lokacin mulkinta Sarauniya Elizabeth ta yi mu'amala da masu rike da sarautun gargajiya, kuma a cewar Alhaji Usman Ado Bayero marigayiyar tana da kyakkyawar alaka da gidan sarautar Kano.

Sarauniya Elizabeth ta mutu ne jiya Alhamis tana da shekara 96 a duniya, bayan ta shafe sama da shekaru 70 tana mulkin kasar Ingila.

Nan da kwanaki tara ne ake sa ran za a binne ta a wani kasaitaccen bikin jana'izar da aka kwashe shekaru ana shiryawa, da zai tattara manyan shugabannin kasashen duniya da dama.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

‘Yan Najeriya Na Juyayin Mutuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta II.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

XS
SM
MD
LG