ABUJA, NIGERIA - Taken taron na wannan shekarar shi ne gina yarda da amana: Na da mahimmanci a bangare samun bayanai da aikin yada labarai da kansa.
Masu ruwa da tsaki da suka hada da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, manyan jiga-jigai daga hukumar bunkasa ilimi, kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya wato UNESCO, mahalarta taro da wasu jiga-jigai daga ciki da wajen Najeriya sun jaddada mahimmancin kirƙirar sababbin hanyoyin da za a bi don magance rashin daidaito wajen tantance sahihan labarai da ma kafofin yadda labarai da samar da ingantaccen ilimi a fannin gano bayanai daga tushe.
Jiga-jigan daga ciki da wajen Najeriyar sun bayyana hakan ne a yayin kaddamar da shirin wayar da kan al’ummar duniya na mako guda a kan aikin jarida da tabbatar da zuba jari a aikin yada sahihan Labarai wato global media and information literacy week da aka fara gudanarwa a birnin tarayyar Najeriya, Abuja a ranar litinin 24 ga watan Oktobar nan.
Dakta Hajjo Sani itace babbar wakiliyar Najeriya a hukumar bunkasa ilimi, kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya mai mazauni a birnin Paris na kasar Faransa wato UNESCO, ta bayyana cewa taron hadin gwiwar wayar da kan al’umma da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta Najeriya da UNESCO suka shirya na da mahicmmancin gaske wajen fadakar da al’umma a kan mai ake nufi da bada karfi wajen tantance sahihancin labarai kafin a fara yadawa.
A cikin mahalarta taron akwai kwamishinonin yada labari daga jihohin Najeriya da dama wadanda suka hada da Zamfara da Filato.
Shima Ali Muhammad daya ne daga cikin dimbim mahalarta taron daga kafaffen yada labarai na cikin Najeriya wanda ya bayyana cewa an maida aikin jarida hawan kawara la’akari da yadda wadanda basu da kwarewa a aikin ke kutsawa ciki.
Akasarin masu ruwa da tsaki a wajen taron dai sun bayyana cewa magance rashin fahimta a sha’anin yada Labaran shi ne mabuɗi don Haɓaka sabbin hanyoyin kawo karshen rashin daidaito wajen tantance kafofin yada labarai da karantar da bayanai
A nasa jawabi a lokacin bude taron, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi fatan za a sami damar tattauna kudurori masu mahimmanci da za su taso a yayin taron da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin duniya, haɓaka karatun yanayin kafofin yada labarai da karantar da bayanai a matsayin cigaba mai inganci don gina amana, kare hakkin zamantakewa, haɗin kai da dai sauransu.
Saurari cikakken rahoton daga Halima Abdulrauf: