Masu ruwa da tsaki a Najeriya, sun ce ya zama wajibi gwamnatin kasar ta ba da fifiko ga bangarorin Ilimi, kiwon lafiya, tsara iyali da kuma fannin sana’o’in al’umma don samun sauki a matsalolin da ake fuskanta a kasar.
Masu ruwa da tsakin sun yi wannan kira ne a yayin wani taron bita da ya gudana a birnin tarayya Abuja na hadin gwiwa tsakanin hukumar kidayar al’umma ta Najeriya wato NPC, babban bankin duniya da kuma ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar da kuma ‘yan jaridu domin neman su ci gaba da ba da gudunmuwarsu.
Taron ya fadakar da 'yan jarida musamman a wajen yin rahotannin farkar da gwamnati a duk matakai kan nauyin da ya rataya a wuyanta da ma wayar da kan al’umma da su tashi tsaye su rika bibiyan al’amurran gwamnati don kawo ci gaban da ake nema a kasar.
A yayin taron dai an ba da mahimmanci ga tunatar da gwamnati a kan gibin da ake samu wajen kasafta kudi ga bangarorin ilimi, kiwon lafiya da ma inganta sana’o’in al’umma a kasar domin samun sauyi a yanayin matsin da ake ciki da kuma rage ko kawo karshen matsalolin da suka addabi kasar ciki da na tsaro.
Tsohon dan majalisar da ya wakilci mazabar Makarfi kudan na jihar Kaduna a tarayyar Najeriya, Hon. Muhammad Usman kuma daya daga cikin mambobin tawagar da suka shirya taron ya ce dole ne gwamnati da yan majalisun kasar su bada fifiko ga fanonnin ilimi, kiwon lafiya, inganta Sana’a don kawo ci gaba mai dorewa a kasar.
Hon. Usman ya kuma kara da cewa ya kamata a saki kudadden da aka warewa bangaren kiwon lafiya musamman fannin tsara iyali na kasafin kudin shekarar 2021 da har yanzu gwamnati bata sake ba don a aiwatar da ayyukan ga al’ummar kasa.
Ko menene mata da ke kan gaba wajen kulawa da iyali ke cewa a game da samun kulawa a fannin kiwon lafiya a Najeriya, Malama Habiba Isa Balarabe, ta ce ba bu abunda talaka ke bukata illa a samawa 'yayansu ilimi da ma kiwon lafiya a halin matsin rayuwa da ake ciki.
Ga abunda Joshua Adams, daya daga cikin ‘yan jaridun da suka halarci taron bitar da aka shirya don hada gwiwa da su ya ce daman dan jarida aikinsa shi ne ya samu ilimi mai zurfi a game da abu don wayar da kan al'umma.
Kusan kullum ‘yan Najeriya na kokawa a game da yadda ake tafiyar da bangarorin kiwon lafiya da ma ilimi a kasar inda masu ruwa da tsaki ke ganin cewa dole ne a sauya salo a samo mafita ga gibin da ake samu don kawo ci gaba da ake bukata a wadannan wurare.
Saurari cikakken rahoton Halima AbdulRa'uf daga Abuja: