Masana kimiyya da fasahar dai sun bayyana hakan ne a yayin taron karrama ‘yan jarida wadanda ke aiki tukuru wajen yada labaran wayar da kan al’umma a kan kayan abinci ‘yan aure da ake gauraya kwayoyin halittunsu kamar su dabba ko tsirrai ta hanyar amfani da dabarun fasahar zamani don yakar matsalolin karancin abinci da fari a Najeriya na Zauren Noma ta fasahar Biotechnology Reshen Najeriya.
Wani rahoton hadin gwiwa da hukumar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya da ma’aikatar noma da raya karkara ta Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki suka fitar ya yi nuni da cewa tsakanin watan Yuni zuwa Agustan shekarar 2022, kimanin mutane miliyan 19 da dubu 400 ne suka fuskanci karancin abinci a fadin Najeriya.
Rahoton dai ya yi nazari ne kan matsalar karancin abinci da abinci mai gina jiki a yankin Sahel da yammacin nahiyar Afirka inda aka gano matsalar abinci za ta shafi dubban 'yan Najeriya a jihohi 21 da birnin tarayya Abuja ciki da 'yan gudun hijira dubu dari hudu da goma sha shida (416,000).
Shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere a jihar Gombe, Farfesa Umaru Pate, ya bayyana cewa 'yan jarida na da muhimmiyar rawa da zasu taka wajen wayar da kan al'umma a game da kayan abinci 'yan aure da ake gauraya halittunsu don rage matsalar karancin abinci a kasa da kuma shirya wa karin al'umma da za a samu a bisa hasashen cewa adadin 'yan Najeriya zai kai miliyan 400 nan da shekarar 2030 .
Dakta Rose Maxwell Gidado dake zaman jagorar zauren kula da aikin Noma ta fasahar Biotechnology Reshen Najeriya ta yi bayani a kan aikinsu a OFAB inda ta ce ‘yan Najeriya sun fara yarda da amfanin gona ‘yan aure kuma ita da iyalanta ma na cin abinci 'yan aure.
Masanin kimiyya a fannin amfani da fasahar Zamani wajen inganta aikin noma na Biotechnology, Mal. Abdulrazak Ibrahim, ya kwantar wa ‘yan Najeriya hankula a kan cewa ana sahihin bincike na tsawon shekaru 13 kan kayan abinci ‘yan aure kafin a fitar don amfanin manoma da sauran al’umma.
Gwarzuwar ‘yar jarida a Najeriya da ta sami lambar yabo da kyaututtuka na kasa baki daya na OFAB a wannan shekarar, Dorcas Bello ta bayyan farin cikinta da nasarar da ta samu tana mai cewa ta ci wake 'yan aure a bainar jama'a don nuna wa masu bibiyan labaran kafar talabijan nasu su amince da cewa kayan abinci 'yan aure basu da illa ga lafiya.
Kayan abinci ‘yan aure wato GMOs sune samfurin abinci wadanda masana kimiyya ke sauyawa kwayoyi ko fasalin halitta ta hanyar amfani da dabarun fasahar hadi ta zamani wanda mutane da dama suka yi imanin cewa abincin GMOs na da illa ga lafiya, saidai masana kimiyya sun ce babu illa ga lafiya da aka tabbatar a halin yanzu.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf: