Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Jiragen Saman Emirates Zai Daina Zuwa Najeriya


Jirgin saman Emirates
Jirgin saman Emirates

Kamfanin jiragen saman jigilan fasinjoji na Emirate yace zai dakatar da aikin jigilan fasinjoji zuwa Najeriya daga ranar 1 ga watan Satumba sakamakon matsalar kin bai wa kamfanin damar daukar kudadensa da ya sayar da tikiti a kasar . 

Kamfanin na Emirate dai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis inda ya ce zai dakatar da jigilar fasinjoji zuwa Najeriya sakamakon yadda ya kasa fitar da kudaden shiga da ya samu a sanadiyar sayar da tikiti wa fasinjojin kasar ta kafar amfani da kudin kasashen waje wato dalar Amurka a maimakon Naira da akasarin mutane ke sayen tikin da su.

Matakin na Emirate na zuwa ne makwanni uku bayan da kamfanin ya aike da wata wasika ga ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Alh. Hadi Sirika, ya na rokonsa da ya sa baki a lamarin don babban bankin kasar wato CBN ya ba wa kamfanin damar fitar da kimanin dala miliyan 85 da suka makale a kasar.

Bayanai dai sun yi nuni da cewa hukumomin Najeriya na son kamfanin ya fitar da kudin a Naira, saboda karancin dala da ake fama da ita a kasar a yanzu.

Tuni dai masu sharhi suka fara tofa albarkacin bakinsu kan tasirin matakin na kamfanin Emirates musamman a sha’anin kasuwanci, cinikayya, karatu da ma neman lafiya, inda Kyaftin Ado Sanusi ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar babban bankin kasar su fitar da tsarin biyan kamfanin na Emirates kudaddensa ko ta zango-zango don kamfanin ya kara yarda da cewa gwamnatin kasar na da aniyar biyan wadannan kudadde.

Shi ma wani masanin sha’anin sufurin jiragen sama Kyaftin Umar Kabo ya bayyana cewa nauyin warware matsalolin maido da kudadden tikitin kamfanin jiragen saman na Emirates zuwa ga lalitar kasar su ya rataya ne a wuyan gwamnatin Najeriya la'akari da yarjejniya da kuma huldar diflomassiya,

Najeriya dai na fama da matsalar karancin kudin kasashen waje musamman dalar Amurka, dalilin kenan da ya sa wasu ke ganin babban bankin Najeriya wato CBN ya dauki matakin hana kamfanonin na jiragen saman kasashen waje damar fitar da kudinsu a dala ko kuma wani kudin na kasar waje.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da kamfanin Emirate ke dakatar da zirga-zirgar fasinjojin daga Najeriya zuwa Dubai da wasu kasashen da ‘yan kasar ke yawaita zuwa don kasuwanci ko kuma neman ilimi a bisa dalili na yaduwar nau’in Omicron na cutar Covid-19 da ma rashin maido da kudadden tikitin da ta sayarwa yan kasar.

A shekarar 2021 sai da kamfanin Emirates ya dakatar da zirga-zirgar fasinjoji zuwa Najeriya na tsawon watanni 10 inda ya sanar da dawo da aikinsa zuwa cikin kasar na kullum a ranar 12 ga watan disambar 2021 din kafin nan aka kara samun sabani daga bisani aka dawo da jigilar fasinjoji a cikin watan Janairun shekarar 2022.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:58 0:00

XS
SM
MD
LG