Manufofin sun hada da samar da zaman lafiya, tsaro, hadin kai da walwala a duniya ta hanyar kawo karshen ta'asar yaki a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice a kasashe kamar Najeriya, Habasha, Ukraine, kudancin Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da dai sauransu.
Masu ruwa da tsakin na Majalisar Dinkin Duniyar dai sun jaddada cewa, Majalisar na kan aiki da manufar da aka kafa ta a kai ta samar da zaman lafiya da ci gaba duk da cewa ya zuwa yanzu ana kan fuskantar yake-yake, rikice-rikice a kasashe kamar su Ukraine, kudancin jamhuriyyar dimokuradiyyar Congo, Najeriya da saura wasu wurare, kamar yadda Dakta Walter Kazadi Mulombo, dake zama wakilin hukumar lafiya ta duniya a Najeriya kuma wakilin babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya inda ya yi kira ga dalibai da suka halarci taron da su rika ziyartar ofishin su a matsayin wadanda a nan gaba zasu zama shuwagabanni don hada gwiwa da su wajen aiki.
A nasa bayanin a lokacin taron na Majalisar Dinkin Duniya, dalibi daga makarantar Premier dake Abuja, Muhammad Nura ya bayyana cewa taron ya kara masa sani a kan ayyukan Majalisar.
A yayin taron, babbar jami’a a asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya-UNFPA, Dakta Rabiah Sageer, ta ce asusun na bada shawarwari da tallafawa aikin wayar da kai a game da tazarar haihuwa, tallafawa mata masu juna biyu, da kuma tallafawa abubuwan da zasu hana cin zarrafin mata.
Taken taron zagayowar ranar da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya na wannan shekara dai shi ne Majalisar Dinkin Duniya da Najeriya - haɗin kai don samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Alkaluman kididdiga dai sun yi nuni da cewa a halin yanzu akwai kasashe mambobi Majalisar Dinkin Duniya 193.
Saurari rahoton cikin sauti: