‘Yan sanda a jihar Maryland da ke nan Amurka sun gano mutumin da ya kashe mutane biyar a ranar Alhamis a kamfanin jaridar Capital Gazette, da ke yankin Annapolis, dauke da gurneti mai hayaki da bindiga.
Shugabannin kungiyar Tarrayar Turai na duba matakan da za su dauka wajen magance matsalar kwararan bakin haure a yayin da suka fara wani taron koli na kwanaki biyu a ranar alhamis.
Jami’ai a Kasar Kenya sun ce wata gobara ta auku a babbar kasuwar birnin Nairobi da safiyar yau Alhamis, har akalla mutane 15 sun mutu, wasu su 70 kuma sun jikkata.
Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasonjo da Shugaban Majalisar Dattawa tare da Gwamnan Jihar Plateau bayan rikicin da ya salwantar da rayyukan al'umma da dama tare da raunata daruruwan mutane.
Yau kwana na 4 kenan da ake cigaba da neman matasa yan wasan kwallon kafa su 12 da mai horaswar su, waddanda ake da tabbacin cewa sun makale a cikin wani Kogo da yayi ambaliya a kasar Thailand.
A makon da ya gabata ne, Trump ya saka hannu kan dokar kin amincewa dukkan bakin haure da kin bari a gurfanar da su tare da tuhumar su, amma ya soke al'adar raba ya'ya da iyayen su.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya Lahadi cewa ya kamata a maida mutanen dake shigowa Amurka ba bisa ka’ida ba kasashen su, ba tare da sa hannun alkalai ko zaman kotu ba.
Yanzu haka an kama mutane 30 dake da alaka da harin da aka kai a Habasha, wanda, Shugaba Abiy ya bayyana a matsayin “shiryayyen hari ne”.
An sake zaben shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasa, inda ya sami fiye da rabin kuri’un da aka kada.
Kasar Italiya ta kafe akan matakin ta na kin ceto ‘’yan ciranin da suka makale a gabar tekunta, ta na mai fadawa kungiyoyin bada agajin kasashen Turai cewa su daina aikin ceto bakin, su bar su dogarawan tekun Libya su kwashe su.
Dan wassan kwallon kafar Najeriya Ahmad Musa, na murna bayan ya saka kwallo biyu a raga a yayin wassan gassar kwallon kafa ta duniya a Rasha tsakanin Najeriya da Kasar Iceland. An tashi biyu da babu a wassan da buga yau 22 ga watan Yuni, 2018. (AP Photo/Darko Vojinovic)
Ofishin Jakadancin Amurka tare da hadin gwiwar hukumar adana kayan tarihi na Waziri Junaidu a jihar Sokoto, sun gudanar da wani taro don inganta harkokin ilimi da gudumawar da mata ke bayarwa.
Fira-Ministar New Zealand din Jacinda Ardern, ta manna hoton diyar da ta haifa a shafinta na Instagram yau Alhamis, tare da mahaifin 'yar Clark Gayford.
Rasha ba ta bata lokaci ba wajen bukatar hanzarin maye gurbin Amurka a Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya.
Akwai alamar an soma shirye-shiryen wani babban taron kolin da ake fatan ganin ya faru a tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa Vladimir Putin na kasar Rasha.
Rahotanni sun nuna cewa gasar cin kofin duniya ta wannan shekarar ta 2018 da yanzu haka ake gudanarwa a Rasha ce gasar cin kofin duniya mafi tsada da aka taba shiryawa.
A halin yanzu hukumar dake lura da al’amuran 'yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya ta ce mutane miliyan 68.5 a fadin duniya aka tilasatawa gudu su bar gidajensu a shekarar data gabata saboda yaki, tashin hankali ko aka tsanantawa.
Domin Kari