Yau Juma’a shugabannin kasashen Turai suka cimma yarjejeniya kan bakin haure.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, “yarjejeniyar labari ne mai kyau”. Kungiyar Turai ce ta fara tattaunawar a jiya Alhamis da yamma aka kuma kammala a safiyar yau Juma’a.
Wananan yarjejeniyar za ta kirkiro wuraren zaman wucin gadi ga masu neman mafaka da ke shigowa daga wasu kasashen zuwa Turai, musamman ga wadanda suka amince da karbar bakin haure.
Sai dai kasar Italiya ta ki amincewa da yarjejeniyar a taron kolin kasashen Turai da ake yi a kasar Brussels, inda suka bukaci kasashen kungiyin 28’ da su kara taimako akan matsalolin bakin haure a birnin Rome.
Firai-Ministan Italiya Giuseppe Conte ya ce, daga baya kasarsa za ta yanke shawarar ko za ta karbi bakunci ko samar da wurin zama na wucen gadi ga bakin haure ko a’a.
Facebook Forum