Yau Litinin babban Jami'in kan iyakar Amurka ya yarda cewa hukumomi yanzu haka baza su iya daukan matakin da gwamnatin shugaba Trump yake so a dauka na dokar kin amincewa a tsare kuma gurfanar da dukkan mutanen da ke shigowa Amurka ba bisa ka'ida ba, yayinda jami'ai ke aikin kirkiro da dokar da zata bari a gurfanar da waddanan mutane ba tare da an raba su da iyalansu ba.
Kwamishinan kwastam da kare kan iyakar kasa Keven McAleena ya fadawa manema labarai a jihar Texas dake nan Amurka cewa, ya daina aika tuhume tuhumen da ake wa iyaye kan shigowar su kasar ba bisa ka'ida ba ga mahukunta, bayan da shugaba Donald Trump ya rattaba hanu kan wata doka a makon da ta gabata da zata dakatar da raba iyaye da ya'yansu bakin haure.
McAleena ya jajirce cewa dokar gwamnatin tana aiki duk da kalubalar da ake fuskanta, ya ce kuma yana aiki kan maido da tuhumar bakin hauren dake shigowa.
Facebook Forum