Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Sake Samun Damar Nada Alkalin Babban Kotun Amurka


Alkali Anthony Kennedy ya sanar zai yi ritaya daga mukaminsa, wanda ke da muhimmanci a kotun kolin Amurka, abinda zai ba shugaba Donald Trump babbar damar nada wani babban alkali karo na biyu a gwamnatinsa, abinda zai kuma share fagen neman cike gurbi mai cike da takaddama da aka dade ba a gani ba a kasa

A cikin shekaru 30 da ya kwashe yana aiki, Kennedy wanda jam’iyyar republican ce ta dora shi kan kujerar ya sha kalubalantar abokan aikinsa masu ra’ayin ‘yan mazan jiya akan jefa kuri’a a wasu muhimman batutuwa a kasar, ciki harda batun zubar da ciki, da ‘yancin masu auren jinsi daya ko canza jinsi, da kuma ‘yancin kada kuri’a. A karshen watan Yuli mai shigowa ne zai daina aikin.

A wata sanarwa, Kennedy dan shekaru 81 da haifuwa, ya ce babban abu ne damar da ya samu wajen yi wa kasa aiki a fannin shari’ar gwamnatin tarayya na tsawon shekaru 43, inda ya yi shekaru 30 a kotun kolin Amurka..”

Shugaba Trump ya ce Kennedy mutum ne mai hangen nesa, ya kuma ce ba tare da bata lokaci ba zai fara neman wanda zai maye gurbinsa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG