Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarrayar Turai Na Duba Matakan Magance Kalubalen Bakin Haure


Shugabannin kungiyar Tarrayar Turai na duba matakan da za su dauka wajen magance matsalar kwararan bakin haure a yayin da suka fara wani taron koli na kwanaki biyu a ranar alhamis.

Yawan zuwa nahiyar ya ragu matuka tun daga rikicin shekarar 2015 da ya janyo rabuwar kawuna tsakanin mambobin kungiyar su 28 akan matakan da ya kamata su dauka. Wasu kasashen sun nemi a a yi amfani da manufofin bude kofa ga bakin, yayinda wasu kuma suka suka dauki matakan hana bakin da suka isa turai tsallakawa zuwa iyakokinsu.

Kungiyar Tarrayar Turan ta ce a shekarar 2015 an samu bakin haure fiye da Miliyan 1 da digo 8 dake tsallakowa iyakar Turai zuwa kasashe ba tare da ka’ida ba zuwa kasashen dake mambobin kungiyar. Shugaban Kungiyar Tarrayar Turai Donald Tusk ya rubuta a wata wasika gabbanin taron kolin cewa yawan masu tsallakowa kashen Turai ba bisa ka’ida ya ragu da kasi 96 cikin 100 tun bayan da abun yayi kamari.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG