Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Italiya Ta Kafe Kan Matakinta Na Kin Ceto Yan Cirani


Kasar Italiya ta kafe akan matakin ta na kin ceto ‘’yan ciranin da suka makale a gabar tekunta, ta na mai fadawa kungiyoyin bada agajin kasashen Turai cewa su daina aikin ceto bakin, su bar su dogarawan tekun Libya su kwashe su.

Ministan harkokin cikin gida na Italiya, Matteo Salvini, ya ce ya kamata hukumomin Libiya su yi aikin su na cetowa, da taimakawa, da kuma maida bakin kasashen su, kamar yadda suka saba yi na tsawon wani lokaci, ba tare da jirgen kungiyoyi masu zaman kansu sun dame su ba ko sun tada wata fitinar, Ya kuma ce “an rufe tashoshin jiragen ruwan Italiya kuma zasu kasance a rufe ga masu taimakawa masu safarar mutane.

Jiya Lahadi, wata ƙungiyar agaji da ake kira Spanish Proactiva Open Arms, ta ce dogarawan tsaron tekun Italiya sun sami sakon gaggawa daga wasu jiragen ruwa guda 6 dauke da kusan mutane 1,000, amma kasar Italiya ta fadawa kungiyoyin agaji irinsu Proactiva cewa kada su damu ba a bukatarsu.

A maimakon aikin ceton, sai dogarawan tsaron bakin tekun Italiya suka sanar da Libya, suka kuma danka aikin ceton ga takwarorin aikinsu na kasar ta Libya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG