Rahotanni sun nuna cewa gasar cin kofin duniya ta wannan shekarar ta 2018 da yanzu haka ake gudanarwa a Rasha ce gasar cin kofin duniya mafi tsada da aka taba shiryawa. Inda aka nuna ce an kashe kudin wuri na gugar wuri akalla Dalar Amurka Miliyan Dubu 15.
An kashe akalla Dala Miliyan Dubu 3 akan ginawa da gyarre-gyaren filayen wasanni guda 12, yayin da kuma aka batar da wasu Dala Miliyan Dubu 8 kan samar da kayan aikin da suka hada da sababbin hanyoyin mota da na jiragen kasa da ma filayen jiragen sama..
A baya dai kasar Brazil ce ta shirya gasar cin kofin duniya na karshe da aka yi kafin wannan da ake yi a kasar ta Rasha, wanda Brazil din ta kashe Dalar Amurka akallah Miliyan Dubu 11 a wancan lokacin na shirya daukar nauyin bakuncin gasar kwallon kafar ta duniya..
Facebook Forum