Yanzu haka ana ta kone-kone a jihar Ceara dake arewa maso gabashin Brazil, an fara tashin hankalin ne kwana daya bayan da aka rantsar da sabon shugaban kasar Jair Bolsonaro.
Yan gudun hijira daga garin Baga sun koka da irin halin da suke ciki, tun lokacin da suka tsere daga garuruwan su zuwa Manguno da babban birnin jihar Borno, Maiduguri. saboda yadda 'yan Boko Haram su ke kona gine-ginan gwamnati dana manyan mutane a garin.
Sojoji dauke da manyan makamai sun rufe ofishin yanki da Hedkwatar kanfanin Jaridar Daily Trust a Biranen Maiduguri da Abuja, kan labarin kwace garin Baga da Jaridar ta ce mayakan Boko Haram sun yi.
Shugaban Amurka Donald Trump yana neman hanyar kawo karshen rufe wadansu ma'aikatun gwamnati duk da yake har yanzu dukan bangarorin sun ja daga kan matsayarsu.
Kungiyar Ahmadiyya wacce ta samo asali daga kasar Pakistan, yanzu haka ta samu karbuwa a fadin Jamhuriyar Nijar, inda tayi taron ta na shekara da ake kira Jalsa Salana da aka bude shi jiya a birnin Konni.
Biyo bayan ganawaa da sanata Linsey Graham yayi da Shugaba Donald Trump, ya ce yana da kwarin gwiwa cewa zai dakatar da aniyarsa ta janye sojojin Amurka daga Syria, wanda hakan zai baiwa Iran damar ci gaba da yiwa Isra'ila Barazana.
Rundunar Sojan saman Najeriya ta kaddamar da tashin jiragenta a filin jirgin saman Sultan Abubakar don tunkarar 'yan bindiga a yankunan jihohin Sokoto da Kebbi, inda ta kara karfin sansaninta na runduna ta 119 dake Jihar Sokoto.
A kalla 'yan kabilar Kambari dubu biyar ne suka halarci taron su na wannnan shekarar, duk da matasalar da yankin nasu yake fama da shi na rashin hanyar motada sauran ababan more rayuwa.
An sake samun wani yaro dan kasar Guatemala da ya mutu yayin da yake tsare a hannun jami’an tsaron kan iyakar kasar Amurka.
Shugaban Kasar Sudan Omar al-Bashir ya yi jawabi ga magoya bayansa a Khartoum, yayinda aka shiga wata sabuwar zanga zanga a babban birnin kasar.
Babban limamin darikar katolika a Demokaradiyyar Jamhuriyar Congo, ya yi kira da babbar murya da a gudanar da zaben 2018 cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba.
A wannan makon kasuwar hada-hadar hannaye jari a Amurka, sun yi mummunar faduwa da ba'a taba ganin irinta ba cikin shekaru goma.
Kasar Ghana tana ci gaba da fuskantar barazana a baya bayan nan sakamakon tashe tashen hankali da ake fuskanta a kasashe dake makwabtaka da ita.
Bana dai Najeriya ta yi bukukuwan kirsimeti cikin walwala da wadatan man fetur, Sabanin yadda ake samun karancin man a shekarun baya.
Sabon sakataran harkokin tsaron Amurka na riko Patrick Shanahan zai fara aiki a ranar daya ga watan Janairu 2019, wanda zai canji Jim Mattis da ya ajiye aikinsa saboda adawa da janye sojojin Amurka daga Syria.
Bakin hauren suna wannan tafiya mai hadari ta cikin sahara na kokarin su na ketarwa zuwa kasashen turai domin samun ingantacciyar rayuwa.
Majalisar limaman Abuja ta bukaci limamai su ci gaba da tsayawa kan gaskiya da gujewa marawa wani bangaren siyasa baya musammanma ganin gabatowar zaben shekarar 2019 dake tafe.
Wasu Dattawa a jihar Kano sun yi kira da babbar murya ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya fito yayi wa mutanan kano bayani akan faifan bidiyo da ake zargin ya nuna shi yana karbar cin hanci daga gurin yan kwangila.
A cigaba da sa'insar da ke faruwa tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyoyi cikin 'yan kwanakin nan, gwamnatin ta ce kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta Amnesty International na ma ta zagon kasa ta fuskar tsaro ta wajen mahaguwar fahimtar salon tsaronta.
Ma'aikatar Kididdiga a Najeriya ta fitar da wasu sababbin alkaluma da ke cewa adadin matasa marasa aikin yi a kasar ya karu daga miliyan 17.6 zuwa 20.9 a 'yan watannin kadan.
Domin Kari