Majalisar limaman babban birnin Najeriya Abuja da ke da kananan hukumomi shida, ta yi gagarumin taro da bita ta wuni biyu don karawa limaman kwarin gwiwar tsayawa kan gaskiya da kaucewa marawa kowanne bangare baya a siyasa.
Majalisar dai ta hada ne da limaman masallatan jumma’a na dukkan kungiyoyin Islama da kan taru a muhimman lokuta duk shekara.
Limamin masallacin jumma’a na Asokoro karkashin ofishin jakadancin Saudiyya, Sheikh Sufyanu Abdullahi shine mataimakin shugaban kungiyar da ke karfafawa limamai su rike duk jama’a da amana da kuma dora su kan gaskiya ba tare da daukar wani bangare ko fifita wani a siyasance ba.
A cikin bayanansu, sun ce samun 'yan takara daga addinai dabam dabam da kuma kalibai dabam dabam manuniya ce kan bukatar ganin an kara karfafa irin wannan hadin kai da fahimtar juna domin ci gaban kasa.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da Cikakken rahoton
Facebook Forum