Bayanin da ma'aikatar Kididdigar ta bayar a Najeriya ya nuna cewa yawan matasa ya karu daga miliyan 111.1 zuwa miliyan 115.4, sannan kuma yawan masu aikin kwadago ya karu daga miliyan 85 zuwa miliyan 90.4, amma kuma yawan masu aikin yi ya karu daga Miliyan 69 zuwa Miliyan 69.5.
Wani abu da Khalid Ismail, matashi kuma dan Jam’iyyar PDP ya ce mahukuntar kasar ne ba su bawa matasa dama. Khalid ya ce gwamnati ta rurrufe bodojin kasar tare da karya aiyukan kwadago wanda ya taimaka wajen nakasa tattalin arzikin kasar. Amma Shugaban Muryar Talaka na Arewa Maso Gabas Saleh Bakoro Sabon Fegi Damaturu, ya ce wannan shaci fadi ne kawai, domin gwamnatin APC a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta kago aiyuka bila'adadin ta hanyar N-Power.
Amma Lauya kuma Kwararre a fanin zamantakewa Mainasara Ibrahim ya ce wadanan alkaluma hannun ka mai sanda aka yi wa gwamnati, saboda ta gyara aiyukan ta domin kuwa mutane na wahala, tunda ba aikin gona kadai ne abinda matasa ke yi a kasar ba.
Shi kuwa Ministan Ma'akatar Matasa da Wassanni Barista Solomon Dalung, ya ce idan an ce gwamnati bata samar da ayyukan yi ga matasa ba to ba a yi mata adalci ba, domin su gyara suka zo yi a kasar kuma su na yi.
Ga cikakken rahoton Medina Dauda ta hada mana
Facebook Forum