Yanzu haka dai Afirka na neman zama dandalin yada labaran karya ko "fake news" kamar yadda ake kira da Turanci. Wadannan labaru sun dade suvna jan hankali game da alaka tsakanin kafafen yada labarai da kuma aikace-aikacen siyasa a kasashe da suka ci gaba a baya-bayannan.
A nan Amurka, fadar White House ta musanta ikirarin da gwamnatin Turkiyya tayi, na cewa shugaba Donald Trump na tunanin mika malamin addinin musulunci nan, Fethullah Gulen ga kasar Turkiyya, malamin da ake nema ruwa-a-jallo.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mutane su taimakawa asusun da ta bude domin tallafawa 'yan gudun hijir Sudan ta Kudu, sama da mutane miliyan biyu da su ke neman agajin gaggawa.