Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Gana Da Shugabannin Majalisa Kan Batun Rufe Ma'aikatun Gwamnati


Ganawar Shugaba Trump da wakilan majalisa
Ganawar Shugaba Trump da wakilan majalisa

Shugaban Amurka Donald Trump yana neman hanyar kawo karshen rufe wadansu ma'aikatun gwamnati duk da yake har yanzu dukan bangarorin sun ja daga kan matsayarsu.

A Yau Laraba ne ake kyatata zaton Shugaba Donald Trump zai gana da shugabannin majalisun tarayyar da ya gayyata zuwa fadar White House a domin ganawa akan harkar tsaron kan iyakar kasar, yayin da wasu ma’aikatun gwmanati su ke a rufe.


Shugaban ya fada a jiya talata cewa, a shirye ya ke daya amince da tattaunawar da zata kawo karshen rufe wasu ma’aikatun gwamnati wanda ya shiga rana ta goma sha daya a sabuwar shekara da muka shiga a jiya daya ga watan Janairu, amma ya dage da cewa duk yarjejeniyar da za a kulla dole ta hada da kudin da za’a gina katanga mai kyau a tsakanin iyakar Amurka da Mexico.


Yanzu haka bayan kwana goma sha daya babu wani ci gaba, shugaban ya nuna alamu cewa a shirye yake ya amince da yarjejeniya a wani sako daya aika ta shafinsa na Twitter.


A ranar Alhamis mai zuwa ne sabuwar majalisar wakilai zata bude, kuma ana kyautata zaton shugabannin ‘yan jam’iyyar Democrat za su gaggauta amincewa da wata doka da zata bada damar sake bude ma’aikatun gwamnati, da dawo da sama da ma’aikatan gwamnatin tarayya 800,000 kan aikin su da kuma biyan su akan lokaci. Sai dai kudaden da ‘yan majalisar na Democrat za su amince da su a cikin dokar, ba za su hada har da kudaden da shugaba Trunp ke nema na gina Katanga a kudancin iyakar Amurka da Mexico ba. Ko da yake babu tabbacin cewa majalisar dattawa za ta amince da dokar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG