Ma’aikatar shige da ficen kasar Ghana, ta shirya taron ta na shekara shekara wa kwamandodin jihohi domin duba cigaba da aka samu da kuma kalubalen da su ke fuskanta.
Ma’aikatar shige da fice ta kasar Ghana a matsayin ta na mai kare iyakokin kasar, tana ci gaba da fuskantar barazana a baya bayan nan sakamakon tashe tashen hankali da ake fuskanta a kasashe dake makwabta abinda ya sa ake neman daukar mataki.
Dalili kenan na shiga wannan taro, kawo yanzu dai an kara wa kwamandodin madafun iko yadda zasu iya bada takardan izini zama cikin kasar na tsawon watanni uku.
Wannan karo taron ya mayar da hankali ne kan bullo da dabaran magance barazanar ‘yan ta'adda, da masu safarar yara, tare kuma da samar da hanyoyin magance su.
A bayaninsa, Shugaban ma’aikatar ta shiga da fice Kwame Asuah Takyi ya ce ba za su yi sake ko su yi kasa a gwiwa ba wajen kare iyakokin kasar domin gudun kada a ayi musu sakiyar da ba ruwa ba.
Da yake tsokaci game da batun, ministan ma’aikatar cikin gida Ambrose Dery cewa yayi akwai bukatar musanyan labarai domin a iya shawo kan barazanar. Ya kuma bayyana cewa, za'a taimaka wa ma’aikatar da kayan aiki da kudi da kuma aiki leken asiri.
Ana sa ran nan ba da jimawa ba za'a gabatar da sabuwar dokar ta 2000 mai lamba 537 da ake kyautata zaton zata taimaka wajen shawo kan kalubalan na tafiye tafiyen mutane da kaya bakin iyakokin kasar.
Saurari cikakken rahoton Ridwan lah Muktar Abbas.
Facebook Forum