Ya kara da cewa, kamata ya yi a dauki ibtila’in da ya faru a ranar Juma’a a New Zealand a matsayin yadda ya zo, wato a matsayin “mummunan aiki na shedanci.”
Ita wannan mahaukaciyar guguwar ta sauka ne a ranar Alhamis a kusa da gabar garin Beira da ke Mozambique, tare da guguwa mai tafiyar kusan kilo mita 200 sa’a guda.
Shugabar masu binciken musabbabin mutuwa, Deborah Marshall, ta ce ofishinta “ya himmatu a ayyukan da yake yi” domin ya tabbatar da an mika kowacce gawa ga ‘yan uwanta.
Yanzu haka an kai hari a wasu Masallatai biyu a kasar New Zealand, 'yan sandan kasar sun kai dauki gaggawa a guraran da abun ya faru.
Biyo bayan hadarin da kamfani jirgin sama na Ethiopia ya yi, kamfani Boeing ya dakatar da saida samfurin jirgin da kamfanin yake kerawa.
Bayan da shugaba Donald Trump ya ayyana dokar ta baci a watan daya gabata don ya yi amfani da karfin ikonsa na shugaban kasa ya gina katanga a tsakanin Amurka da Mexico, majalisun kasar sun ki amincewa da ita.
Bayan da hukumar zaben Najeriya ta fitar da sanarwar ranar da za a gudanar da zabukan da ba a kammala ba, jam'iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP, kowacce ta nuna kwarin gwiwar cewa ita za ta samu nasara.
An gurfanar da wasu shahararrun mutane 50 a gaban kotu, saboda wata badakala mafi girma ta bada kudi domin shiga wasu manyan makarantu a Amurka.
Yanzu haka kasashen duniya da dama sun bada umarnin hana amfani da irin wannan jirgi na Boeing 737-Max 8. tun bayan da irinsa ya fadi a kasar Habasha a satin da ya gabata.
Wasu mata magoya bayan dan takarar gwamana na jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, Bala Muhammad Duguri (Kauran Bauchi), sun yi wata zanga zangar lumana a kan titin zuwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta reshen jihar.
Biyo bayan nasarar lashe zaben da gwamnan jihar Taraba, Akitek Darius Dickson Isiyaku na PDP ya yi, yanzu haka wata sabuwa ta kunno kai inda dan takarar APC a jihar ya ce ba zata sabu ba.
Najeriya ta tura jami'anta zuwa Indiya domin su dauko tsarin da ta bi na magance matsalar bahaya a fili da mutanenta miliyan 500 su ke yi.
Yanzu haka 'yan kasashe 35 hadarin jirgin saman Habasha ya rutsa da su, inda fasinjoji 157 suka rasa rayukansu.
Wasu wadanda ba'a san ko su waye ba, sun kai hari kan cibyar masu kula da cutar Ebola da ke kasar Congo, inda suka hallaka dan sanda daya.
Yanzu haka muhawara ta kaure a Amurka akan launin fata ko matsayi kan irin tasirinsu a wajen yanke hukunci da masu shari'a su ke yi a kasar.
Yanzu haka kotun daukaka kara da ke Yola ta bai wa dan takarar jam'iyyar APC damar shiga zaben gwamna a jihar Taraba da za a gudanar a gobe Asabar.
Ana ci gaba da takaddama game da hakikanin mutumin da zai yi wa jam'iyyar PDP takarar gwamana a jihar Kano bayan da wata kotu ta jingine hukuncin hana Abba Kabiru Yusuf tsayawa takara a zaben da ke tafe.
Tub bayan da jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Adamawa ta gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar wanda zai tsaya mata takarar gwamna, jam'iyyar ta rabe gida biyu, inda wasu su ke gani ayi "SAK" wasu kuma na ganin a zabi cancanta.
A Najeriya, an shigar da hukumar zabe ta INEC da kuma Jam'iyyar ADP kara a gaban kotun tarayya da ke Minna babban birnin jihar Naija.
Domin Kari