Hukuncin shekaru hudu na zaman gidan yari da Alkalin wata kotun tarayya ya yankewa Paul Manafort, na ci gaba da shan suka daga wasu bangarorin al’umar Amurka, wadanda suka kwatanta hukuncin a matsayin “rainin hankali.”
Wannan hukunci ya zo wa mutane da dama a ba-zata.
Hukuncin ya farfado da wata dadaddiyar muhawara da aka jima ana yi, kan yadda launin fata ko matsayi ke tasiri a fannin shari’ar Amurka.
A ranar Alhamis da ta gabata, Alkali T.S Ellis na kotun Gunduma, ya yanke hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 47 ga Manafort, watanni bayan da aka samu tsohon shugaban kwamitin yakin neman zaben na Trump da laifi.
An sami Manafort da laifin kaucewa biyan haraji da damfara kan wasu kudade da ya samu, a lokacin yana yi wa wasu ‘yan siyasar kasar Ukraine aiki.
Wasu na ganin, Alkalin ya nuna matukar sassauci a hukuncin, wanda masu shigar da kara da farko suka nemi a yanke mai hukuncin shekaru 19.5 zuwa 25, kamar yadda dokar yanke hukunci ta tarayya ta tanada.
Amma Alkalin ya ce shekarun sun yi tsauri da yawa.
Facebook Forum