Bayan wani hari da aka kai a yankin Kashmir da ke karkashin ikon India, wanda ya hallaka mutane da dama, yanzu haka Pakistan ta ba da sanarwar damke shugaban kungiyar da ake zargi da kai harin.
Trump ya shiga nuna matukar bacin ransa game da takardun neman bayanai da kwamitin shari'a na majalisar wakilai karkashin Jerrold Nadler su ka aika ga wasu makusantansa da zummar bincikensa.
Yanzu haka ana gudanar da wani taron koyawa matasa ayyukan yi a Jamhuriyar Nijar, domin a canja tunaninsu wajen yin tafiya mai hadari da su ke yi zuwa kasashen Turai, inda su ke rasa rayukansu a cikin Sahara ko Teku.
Yanzu haka kan 'yan jam'iyyar APC a jihar Adamawa ya rabu biyu, inda wasu magoya bayan shugaba Buhari su ka ce ba za su yi SAK ba, za su zabi cancanta ne a zaben gwamna da za'a yi ranar Asabar
Falasdinawa na adawa da wannan mataki na Amurka, domin a cewarsu, dauke ofishin jakadancin daga Tel Aviv zuwa Birnin Qudus, na nuni da cewa Qudus ya zama babban birnin Isra’ila.
Shugaban kwamitin yakin neman zaben Bouteflika, Abdelghani Zaalane ya ce shugaban zai sake kiran wani sabon zabe a cikin shekara daya idan ya lashe zabe a karo na biyar.
Dakarun da ke samun goyon bayan Amurka, sun bayyana cewa samun karin fararen hula a yankin, wadanda mayakan ke amfani da su a matsayin garkuwa, shi ne dalilin da ya sa farmakin ke tafiyar hawainiya.
Yanzu 'yan takara hudu ne suke kalubalantar shugaban kasar Senegal Macky Salls a Zaben shugaban kasar da aka yi jiya Lahadi, cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yanzu haka ana ci gaba da kidayar kuri'un da aka jefa a ranar Asabar a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun a Najeriya.
Yan sanda sun kama Christopher Paul Hasson ne a makon daya gabata da zargin mu'ammala da miyagun kwayoyi da makamai, inda daga baya suka gano shirinsa na kai hari kan wasu 'yan Democrat da kuma 'yan Jaridu.
Kasar Afrika ta Kudu ta amice ta mika tsohon ministan kudin kasar Mozambique ga kasar sa domin ya fuskanci shari'a.
Hadakar kungiyoyi a jihar Taraba ta koka da tura karin sojoji a jihar, saboda fargabar da mutane suka shiga a shirye shiryen zaben da za a yi gobe.
A cigaba da daukar matakan tsaro da rundunar 'yansandan Najeriya ke yi, Sfeto-Janar din 'yansandan Najeriya Mohammed Adamu ya shawarci duk wani mai bindiga ya mika ta ga hukumar kafin ta je karbowa da kanta.
Yanzu haka akalla jihohi goma sha shida su ka shigar da Trump kara a kotun tarayya da ke JIhar California, amma shugaba Trump ya ce yana da ikon ayyana dokar ta-baci domin ya gina katanga a kudancin Amurka da Mexico.
shugaban sojojin kasar Venezuela ya sake jaddada goyon bayan su da shugaba Nicolas Maduro, biyo bayan kalaman da Shugaba Trump ya yi akan kasar ta su.
Yayin da Najeriya ke fuskantar zabe a ranar Asabar mai zuwa, rundunar soji ta shida da ke Fatakol a jihar Rivers, sun gano ana shirin yin amfani da wasu bata gari domin ta da hankalin masu jefa kuri'a ranar zabe.
yanzu haka ofishin ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar ya bukaci gwamnan jihar Tilabery da ya janye dokar ta-baci da ya kafa a jihar.
Tshohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shi zai lashe zaben shugaban kasa da za'a yi ranar Asabar mai zuwa.
Kamar yadda aka san na iya faruwa, hidiman Shugaban Amurka Donald Trump na kare ayyana dokar ta baci da ya yi, su na masu nuni da illar rashin yin hakan.
Domin Kari