Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Sun Yi Zanga-Zanga Kan Makomar Zaben Gwamnan Bauchi


Wasu mata magoya bayan dan takarar gwamana na jam'iyyar PDP a jihar Bauchi, Bala Muhammad Duguri (Kauran Bauchi), sun yi wata zanga zangar lumana a kan titin zuwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta reshen jihar.

Daruruwan mata sun gudanar da zanga zangar lumana a jihar Bauchi jiya Talata, inda suka dirfafi ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da niyyar toshe kofar shiga hukumar zaben, amma jami’an tsaro da aka jibge don saka ido kan masu kai-komo sun hana matan isa ofishin.

Sai dai jami’an tsaron sun bar matan sun gudanar da zanga zangar ta lumana a dab da kwanar shiga ofishin hukumar zaben.

Wasu daga cikin matan na bayyana cewa sun zabi abinda su ke so amma an hana su, don haka suna mika kukansu da shugaba Muhammadu Buhari, da ya sa a bayyana sakamakon zaben jihar.

Sakataran yada labaran jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Alhaji Yahaya Nuhu Gabari, ya ce kamar yadda kowa ya sani an yi zaben gwamna ranar 9 ga watan Maris, kuma jam’iyyar PDP ta samu rinjaye wanda ya kamata a tabbatar da wannan zaben cewa, Bala Muhammad Kaura, shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar.

Sannan kuma ya yi zargin cewa an yi amfani da wasu dalilai ba bisa ka’ida ba aka ki saka musu kuru’unsu na karamar hukumar Tafawa Balewa.

A martanin da jam’iyyar APC ta mayar ta hannun sakataran kwamitin yada labarai na yakin neman zaben gwamnan jihar, Balarabe Shehu Illela, ya ce matsayin su dan gane da soke zaben, suna da kwarin gwiwar su za su lashe zaben da za a sake gudanarwa.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammada:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG