Fadar Gwamnatin Amurka ta White House, ta yi watsi da duk wani yunkurin da ake yi na alakanta shugaba Donald Trump da mai rajin ganin an fifita farar fatan nan da ya bindige mutum 50 a wasu masallatai biyu da ke kasar New Zealand.
Mukaddashin shugaban ma’aikatan fadar, Mick Mulvaney, ya fadawa gidan talbijin na Fox News a jiya Lahadi cewa, “shugaba Trump ba mai irin wannan akida ba ne ta ganin an fifita farar fata,” yana mai cewa “ban san so nawa za mu ta nanata hakan ba.”
Ya kara da cewa, kamata ya yi a dauki ibtila’in da ya faru a ranar Juma’a a New Zealand a matsayin yadda ya zo, wato a matsayin “mummunan aiki na shedanci.”
Dan bindigar da ake zargi da kisa, Brenton Harris Tarrant mai shekaru 28 wanda dan asalin kasar Australia ne, ya yi wani rubutu mai shafi 74, wanda ya fitar jim kadan kafin ya kai harin a wasu masallatai da ke unguwar Christchurch.
A rubutun, Tarrant ya bayyana cewa, yana kallon shugaba Trump a matsayin wani “sabon jagoran fito da manufofin fararen fata,” amma ya ce ba ya goyon bayan tsare-tsarensa.
Wannan sanarwa da Tarrant ya fitar, ta kara farfado da sukar da ake wa shugaba Trump cewa, ya ki ya fito fili ya yi Allah wadai da masu fafutukar ganin an fifita jinsin farar fata ba.
Facebook Forum