Gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amurka na kokarin jan kafa kan kiraye-kirayen da ake dada yi a cikin kasar da kuma waje, cewa ta ba da umurnin dakatar da amfani da wasu sabbin jiragen sama samfurin jet, wadanda sau biyu irinsu ke rikitowa cikin watanni shida kawai, har aka samu mutuwar mutane 350.
A cewar wasu hadiman Fadar Shugaban Amurka ta White House, Shugaba Trump ya shiga tattaunawa kan matsalar ta jirgin sama samfurin Boeing 737-Max 8, tare da wasu mutane wadanda hadiman ba su fayyace ba.
Tun da farko a jiya Talata, Shugaba Trump ya samu tabbaci daga shugaban kamfanin da ke kera jirgin na Boeing 737-Max 8 cewa jirgin bai da matsala, a cewar wasu jami’an kamfanin na Boeing.
Tun bayan da irin wannan jirgin ya fadi ranar Lahadi a kasar Habasha, hukumomin tasoshin jiragen kasashe da dama a fadin duniya, ciki har da China da Turkiyya da Indonesia da Brazil da Koriya Ta Kudu da kuma daukacin kasashen da ke cikin kunkiyar Tarayyar Turai (EU) su ka ba da umurnin hana amfani da irin wannan jirgi na Boeing 737-Max 8, al’amarin da ya mai da shi samfurin jirgin sama mafi bakin jini a duniya.
Facebook Forum