A ranar Litinin da ta gabata babbar kotun tarayya ta haramta takarar gwamnan Kano da Engr. Abbab Kabiru Yusuf, karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, saboda keta sharrudan zabe wajen tsayar da shi takara.
Sai dai rashin gamsuwa da wannan hukunci ya sanya bangaren mutumin da aka ayyana a matsayin dan takara, suka garzaya kotun daukaka kara da ke Kaduna.
Tun da fari, Alhaji Ibrahim Ali Amin, daya daga cikin wadanda suka nemi takarar gwamnan na Kano a inuwar jam’iyyar PDP, shi ne ya shigar da kara gaban babbar kotun tarayya da ke Kano, wanda ya nemi a haramta duk wani dan takara da aka kawo daga Kano a karkashin jam’iyyar PDP.
Sai dai a zamanta na Jiya game da lamarin, kotun daukaka kara da ke Kaduna ta ba da umarnin jingine wancan hukunci na babbar kotun tarayya ta Kano.
Shi ma jagoran kungiyar kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya yi tsaiwar irin ta daka domin ganin Abba K Yusuf, ya samu takarar gwamnma a karkashin jam’iyyar PDP, ya ce sun ji dadin wannan hukunci da kotun daukaka kara ta yanke, don haka duk wanda yake da ja to ya daukaka kara.
Ga alama dai tsugune ba ta kare game da wannan takaddama domin kuwa, Alhaji Ibrahim Ali Amin, ya ce a yau Juma’a zai garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta Kaduna ta yi.
Kwamishinan hukumar zabe na kasa reshen jihar Kano, Farfesa Risqua Arab Shehu, ya ce duk abind a kotu ta aikowa hukumar zabe da shi za ta yi.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
Facebook Forum