Yayin da a baya shugaba Trump ya ke yawan cewa ana kwarar Amurka a kungiyar Tsaro ta Nato, yanzu kuma ya shiga yabon kungiyar saboda sun amince za su kara irin gudunmuwar da su ke bayarwa.
Bayan da kotun soja da ke zama a Garin Maiduguri, hedikwatar jahar Borno, ta samu sojan sama Flight Lt. Matins Enweran da laifin aika ta fyade ga wata yarinya 'yar shekaru 14 kuma yar gudun hijra da ke zaune a sansanin Bakasi, kotun ta kore shi daga aikin soja tare da rage masa mukami.
Shugabanin addinai da ke jihar Taraba sun yi kira da gwamnatin jihar da ta tarayya da su dauki matakan magance matsalar satar mutane da ta addabi wasu yankuna a jihar musamman yanki Tukum da Lau.
A cigaba da murza gashin bakin da ake yi tsakanin Amurka da kasar Mekziko saboda zargin barin bakin haure da ratsawa da kasar zuwa cikin Amurka, Shugaba Donald Trump ya ce Mekziko ta hana bakin hauren ko kuma a sake lale.
Kiran na zuwa ne bayan da jami'an tsaron China su ke kamawa tare da tsare wasu mabiya addinai, da kuma zargin azabtar da su, a wasu lokutanma harda rushe musu guraren ibada.
Bayan da Babban mai shari'ar Amurka, William Barr, ya fitar da takaitaccen bayani kan rahoton Mueller a shafi hudu, yanzu haka 'yan jam'iyyar Dimokrat sun bukace shi daya fitar da cikaken rahoton mai shafi sama da dari uku.
Garkame al'ummar musulmi musamman 'yan kabilar Uighur da sauran tsirarun al'ummomin musulmai da China ta ke yi a wasu sansanoni, ya ja hankalin Amurka, wadda ta yi tir da hakan, tare da kiran China ta daina.
Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin bincike na musamman na Robert Mueller ya mika sakamakon rahotonsa, inda ya ce ba a ga shaidar cewa kwamitin yakin neman zaben Trump na shekarar 2016 ya hada baki da Rasha ba.
Yanzu haka bayan da babbar kotun jihar Adamawa ta janye umarnin da ta baiwa hukumar zabe na ta dakatar da kammala zaben gwamnan jihar, hukumar zaben ta INEC ta shirya gudanar da kammala zaben ranar Alhamis 28 ga watan Maris.
Yanzu haka wani rahoto da masu saka ido daga kungiyar Tarayyar Turai (E.U.) suka fitar ya yi zargin cewa an ci zarafin masu jefa kuri'a tare da firgita su a zaben gwamnoni da aka kammala a jihohin Bauchi, Biniwai, da kuma Kano.
Ma’aikatan Viking Sky sun aika da yakuwar neman taimako a ranar Asabar lokacin da injin din jirgin ya lalace.
Masu ayyukan ba da agaji sun ce tabbas adadin mutanen da suka mutu a kasashen uku zai karu, yayin da ambaliyar ruwan ke janyewa.
Amma dangane da ko shugaba Trump ya yi kokarin kawo cikas ga binciken da kwamitin na Mueller ke yi, Barr ya bayyana cewa, “rahoton bai dauki matsaya ba, kan ko shugaban ya aikata laifi, sannan kuma bai wanke shi ba.”
Wata sanarwa da shugabar kungiyar ta Red Cross a Mozambique Jamie LeSueur ta fitar, ta nuna cewa masu ayyukan agaji sun fi damuwa barkewar cututtuakan da akan samu daga ruwa, tana mai fatan matakan gaggawa da aka dauka, za su dakile aukuwar hakan.
Bayan da wata babbar kotu a jihar Adamawa ta ba da umarnin dakatar da zaben jihar da za a kammala, hukumar zaben ta INEC reshen jihar ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar wannan hukunci.
Yanzu haka an yanke wa babban limamin Cocin Katolika na Faransa hukuncin daurin watannin shida, saboda kin sanar da hukumomi laifin lalata da wani Firist ya aikata.
Bayan wasu shekaru da dama, yanzu haka kasar Brazil da Amurka sun bude wani sabon shafi na hulda tsakanin kasashen biyu mafiya girma a yammacin duniya.
Masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sun addabi yankin Takum da kuma sauran kananan hukumomin jihar Taraba, inda su ka yi awon gaba da mutane da dama wadanda kawo yanzu ba a san inda su ke ba.
Bayan dogon lokaci da kungiyoyin kwadago suka dauka suna neman majalisun Najeriya su amince da kudirin dokar mafi karanci albashi ta Naira 30,000, yanzu haka majalisun sun amince.
Domin Kari