Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Duniya Na Tir Da Karairayin Kafafen Labaran Amurka


Shugaba Trump
Shugaba Trump

Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin bincike na musamman na Robert Mueller ya mika sakamakon rahotonsa, inda ya ce ba a ga shaidar cewa kwamitin yakin neman zaben Trump na shekarar 2016 ya hada baki da Rasha ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi hasashe jiya Talata cewa, duniya baki daya na yin Allah wadai da manyan kafafen labaran Amurka, saboda yadda su ka yi ta yada abin da ya kira, “almarar cewa an yi hadin baki da Rasha.”

“Manyan kafafen yada labaran na shan caccaka da ba’a a fadin duniya, inda ake kiransu gurbatattu kuma makaryata,” a cewar Trump ta kafar witter. Ya kara da cewa, “Sun shafe shekaru biyu su na ta yada almarar nan ta cewa, an yi hadin baki da Rasha, alhalin kuwa a duk tsawon lokutan nan sun san cewa babu wani hadin baki da aka yi.

Su ne makiya jama’a na hakika, kuma su ne jam’iyyar adawa a zahiri.”

Trump ya sake tura sakon twitter din wasu magaya bayansa mai cewa, tun asali ma bai kamata a yi wannan binciken da aka shafe tsawon watanni 22 ana yi karkashin Mai Bincike Na Musamman Robert Mueller ba.

To amma, a gefe guda kuma, ganin cewa Mueller ya cimma matsayar cewa babu shaidar an yi hadin baki da Rasha, sai Trump ya ce, “Rahoton Mueller din mashahuri ne. Kuma ya na da matukar inganci.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG