Yanzu haka jama’ar Jihar Taraba na barci da ido daya a bude, sakamakon matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a jihar, lamarin da ke hana jama’a kwana a gidajensu.
Kuma wannan matsalar tafi Kamari ne a yankin Takum da kuma wasu kananan hukumomin jihar.
Wani mazaunin yankin Takum ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane goma sha biyar a yankin nasu, ciki har da wani mai gidan mai da aka yi garkuwa da shi sati biyar da suka shige, inda masu garkuwar suka nemi a basu Naira miliyan dari domin su sako shi.
Kamar yadda wani mazaunin yankin na Takum ya tabbatar, an ba wa masu garkuwa da mutane kudin amma daga bisani sun nemi a kara musu adadin kudin da suka karba tun da farko.
Shugaban kungiyar kare hakkin dan’adam na jihar Taraba, Kwamared Gambo Dawud, ya ce wannan garkuwa da mutane da ake yi domin neman kudin fansa yana damunsu, sannan ya yi kira da gwamnatin jihar Taraba da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya da su dau mataki domin magance wannan matsala da ta addabi mutanen jihar.
Shima kwamishinan ‘yan sandan jihar Taraba, Alkassim Usman, ya kira taron manema labarai inda ya nuna wasu da aka kama da ake zargi masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu, a karkashin Ofireshan Cika Aiki da rundunar ta fara.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz:
Facebook Forum