Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Democrat Sun Bukaci Barr Ya Fitar Da Cikakken Rahoton Mueller


Bayan da Babban mai shari'ar Amurka, William Barr, ya fitar da takaitaccen bayani kan rahoton Mueller a shafi hudu, yanzu haka 'yan jam'iyyar Dimokrat sun bukace shi daya fitar da cikaken rahoton mai shafi sama da dari uku.

Yayin da jami’ai a Amurka suka bayyana cewa, rahoton da kwamitin Robert Mueller da ya gudanar da bincike kan katsalandan din da Rasha ta yi a zaben 2016, ya haura sama da shafi 300, ‘yan Jami’yyar Dimokrat sun gabatar da wata sabuwar bukata ta neman Atoni – Janar William Barr ya fitar da cikakken rahoton baki dayansa.

Bukatar da ‘yan Dimokrat din suka mika, na zuwa ne bayan da Barr ya fitar da takaitaccen bayani kan rahoton a shafi hudu.

“Ku nuna mana rahoton” shugabar masu rinjaye ta majalisar wakilai, Nancy Pelocy ta ce, tana mai kira da babban jami’in shari’ar kasar.

Ta kara da cewa “ba ma bukatar ka yi mana tafinta. Dole ne mu ga hakikanin bayanan da rahoton ya kunsa. Ba ma bukatar Antoni Janar ya mana tafinta kan wani abu da zai nuna mana kawai.”

A cikin takaitaccen bayanin da ya fitar, Barr, ya yi amfani da kalmomi 65 ne kawai daga cikin rahoton na Mueller, ko da yake, ya kawo misalai kan wasu batutuwa da masu shigar da kara suka tattaro.

A wata wasika da aka aikawa shugabanin majalisu kuma aka fitar da ita a bainar jama’a, Barr ya ce, Mueller ya gano cewa, shugaban Amurka, Donald Trump, da kwamitin yakin neman zabensa ba su hada kai da Rasha ba domin taimaka masa ya lashe zabe, amma kuma bai ce komai ba dangane ko Trump, a lokacin da yake shugaban kasa ya yi katsalandan a harkar shari’a a kokarin da yake na hana binciken.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG