Babbar kotun jihar Adamawa da ke zamanta a Yola ta janye umarninta na farko da ya hana hukumar zabe ta INEC kammala zaben gwamnan jihar.
Yanzu haka hukumar zaben ta INEC ta tsaida gobe Alhamis 28 ga watan Maris a matsayin ranar da za a kammala zaben gwamnan jihar.
Kwamishinan zabe na INEC reshen jihar Adamawa, Barrista Kassim Gana Gaidam, ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da zaben cikin nasara.
Tuni babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma dan takararta, Ahmadu Umaru Fintiri, suka ce sun shirya domin shiga zaben na gobe tare da kiran magoya bayansu da su fito domin jefa kuri’unsu.
Sai dai a martanin da jam’iyyar APC, ta yi fatali da wannan rana ta Alhamis, inda sakataran tsaretsarenta, Ahmad Lawal, ya zargi hukumar zabe ta INEC da marawa 'yan adawa baya.
Tun da farko dai kotu a karkashin mai shari’a, Abdul-Aziz Waziri, ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron karar da jam’iyyar MRDD ta kai hukumar zabe ta INEC gaban ta na rashin saka tambari ko alamar jam’iyyar a takardar kada kuri’a.
Sannan kotun ta ajiye jiya Laraba don sauraron bukatar jam’iyyar MRDD da ta bukaci kotu ta soke zaben da aka yi na ranar 9 ga watan Maris.
Amma alkalin kotun ya ce zai yanke hukunci a ranar Juma’a 29 ga watan Maris din nan.
Saurari cikakken rahoton Abdul-Aziz Ibrahim daga Yola:
Facebook Forum