Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Fada Da Addini - Inji Jakadan Amurka


Kiran na zuwa ne bayan da jami'an tsaron China su ke kamawa tare da tsare wasu mabiya addinai, da kuma zargin azabtar da su, a wasu lokutanma harda rushe musu guraren ibada.

Wani babban jami’in diplomasiyyar Amurka da ke kare ‘yancin yin addini, ya yi kira ga China da ta dakatar muzgunawar da take wa wasu mabiya addini.

Jakadan Amurka kan ‘yan cin yin addini na kasa da kasa, Sam Brownback, ya fadawa ‘yan jarida cewa “China tana fada ne tare da addini, amma wannan fadan ba za su yi nasara ba.”

“Jam’iyyar Kwaminisanci ta China ba ta amince ta kyale mutanenta su zabi abin da suke ganin turba ce mai kyau ga rayukansu, muna magana ne akan al’umar da jama’arta, ta haura biliyan daya, inji Brownback.

Ya kuma kara da cewa, wannan tafarki da hukumomin na China suka dauka, na nufin Musulmai ba za su iya ci gaba da sawa ‘ya’yansu suna irinsu Mohammed, sannan su ma mutanen Tibet da ke bin addinin Bhudda ba za su iya zaba ko su girmama sunayen shugabanninsu ba, kamar yadda suka saba yi na tsawon shekaru sama da dubu.

Brownback ya kara da cewa, anata lalata coci-coci sannan ana tilastawa wasu suna dasa na’urorin daukan hoto na sirri.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG