Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya bayyana garkame al’ummar Musulmi, akasari ‘yan kabilar Uighur, da sauran tsirarun al’ummomi Musulmi, da kasar China ta yi a wasu sansanonin da ke yankin Xinjiang na yammacin kasar, da cewa abin tayar da hankali ne kuma na yin Allah wadai.
“Mun sha fitowa fili mu na yin tir da hakan, kuma mun yi ta tattaunawa da China a kebance kan wannan batu,” a cewar Pompeo yayin da ya ke amsa tambayar da Muryar Amurka ta masa kan batun.
Ya kara da cewa Amurka na kan kokarin shawo kan China ta gane cewa hakan bai dace ba, kuma ta daina.
Dama kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi kasar ta China da garkame miliyoyin ‘yan kabilar Uighurs.
A martaninta, China ta ce shirin kawar da tsaurin ra’ayi ta ke yi, kuma ana koyar da ayyukan yi da doka da kuma harshen Sin na Mandarin a sansanonin.
Facebook Forum