Wannan mataki da Amurka ta dauka ya biyo bayan gargadin da ta yi ma kasar iran kan cewa ta na baraza ga muradunta da kuma na kawayenta.
A yau ake bikin ranar 'yan jarida ta duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, sai dai har yanzu 'yan jaridu na fuskantar kalubale musamman a kasashe masu tasowa. Wasu 'yan jarida a Najeriya sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta.
Yarima mai jiran gado Naruhito zai zama sabon sarki lokacin da wa’adin mulkin Akihito a hukumance zai kawo karshe a tsakar daren yau.
Bayan da aka sanar da zaben raba gardamar da aka yi a Masar, yanzu haka mutanen kasar sun amince da a yi wa kundin tsarin mulkin kasar garanbawul da zai bai wa shugaban kasar dama zama akan karagar mulki har zuwa 2030.
Kotun kolin Amurka ta amincewa gwamnatin Trump ta saka tambayar ko mutum dan kasa ne ko kuma ba dan kasa ba ne, abin da ake ganin zai iya hana baki shiga shirin kidayar da za a yi a shekarar 2020.
A wani sako da ta aika a shafinta na Twitter, IS ta bayyan cewa hare-haren Sri Lanka da ya hallaka sama da mutane 300 tare da jikkita wasu sama da 500, cikin su har da wasu yan kasashen waje 38, martani ne ga kasashen da suka hada kai su ka yi galaba akanta a Siriya.
A wani al'amari mai ban mamaki, wani matashi dan wasan barkwanci, wanda bai da wata gogewa a siyasance, mai suna Volodymyr Zelenskiy, ya yi mummunan ka da Shugaba Petro Poroshenko a zaben Shugaban kasa.
Tun bayan da Turkiyya ta sayi wasu kayan yaki daga Rasha, aka shiga cacar baka tsakanin Amurka da kasar, inda Amurka ta ke ganin Turkiyya na barazana ga kungiyar tsaro ta NATO.
Tun bayan da 'yan majalisun kasar Masar su ka amince da karin wa'adin shugaban kasar na ci gaba da zama a ofshinsa har zuwa 2030, yanzu haka al'ummar kasar da ke ciki da wajen kasar suma za su kada kuri'unsu kan lamarin.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkar tsaro, ya bayyana cewa kasashe uku na yankin Latin Amurka za su fuskanci karin wasu takunkumai.
Shugaban Faransa ya yi alkawarin sake gina Cocin nan mai dumbin tarihi da ke Paris a cikin shekaru biyar masu zuwa, ya kuma fadi hakan ne ta gidan talabijin din kasar a lokacin da yake wa mutan kasar jawabi.
A makon daya gabata ne dai sojojin kasar Sudan suka hambarar da dadaddan shugaban kasar Omar al-Bashir, sakamakon zanga zanga da ta yi kamari. yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojojin da su mika mulki ga farar hula cikin kwanaki 15.
Yanzu haka mutanan da suke zirga zirga daga Kaduna zuwa Abuja ta jirgin kasa, sun koka saboda wahalar da suke sha wajan siyan tikitin jirgin sakamakon yawan mutane da suke bukatar siyan sa.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev. Dr. Samson Ayekunle, ya kai ziyar sansanin 'yan gudun hijira na Cocin EYN a unguwar Wulari da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda ya ba da tallafi ga 'yan gudun hijirar da ke sansanin.
A cigaba da kikikakar da ake yi bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a Sudan, masu zanga-zanga sun ce muddun wayon-aci sojoji su ka yi da sunan juyin mulki, to su ma za a masu zanga-zanga har sai sun sauka.
Yayin da bangarori ke ta barin wuta kan juna a kasar Libiya ta yadda farar hula ke fama, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangaren Janar Khalifa Haftar bangaren gwamnati da su kwance damara.
An dai shirya ficewa Birtaniya a ranar 29 ga watan Maris, amma May ta samu amincewar daga tarayyar Turai na dan wani karamin karin lokaci da zai bai wa gwamnatin dama ta samu mafita da 'yan majalisar kasar za su amince.
Bayan da aka shafe tsawon lokaci ana ta zanga zangar bijire ma dadaddan shugaban Algeriya Abdul'aziz Bouteflika don ya sauka daga kan karagar mulki, shugaban ya bada kai bori ya hau inda ya mika takardar ajiye aiki.
Domin Kari