Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Tayi Nasara A Kotun Kolin Amurka Kan Tambayar Kidaya


Kotun kolin Amurka ta amincewa gwamnatin Trump ta saka tambayar ko mutum dan kasa ne ko kuma ba dan kasa ba ne, abin da ake ganin zai iya hana baki shiga shirin kidayar da za a yi a shekarar 2020.

Alkalan kotun kolin Amurka, masu ra’ayin mazan jiya, wadanda kuma su ke da rinjaye a kotun, sun goyi bayan shugaba Donald Trump, kan bukatar da gwamnatinsa ta gabatar, na neman a saka tambayar neman sanin asalin kasar mutum, a cikin jerin tambayoyin da za a yi wa mutane a shirin kidayar jama’a da za a yi a badi, duk da cewa wasu manyan jihohin kasar da birane, sun dasa alamar tambaya kan wannan bukata, wacce suka ce, za ta iya hana baki shiga shirin na kidayar jama’a, wanda ake yi a duk shekaru goma.

Alkalai biyar da suka fi yawa a kotun mai alkalai tara, sun rinjayi sauran takwarorin aikinsu, a wani zaman taro da suka yi na tsawon sama da sa’a guda, inda suka kalubalanci matsayar da marasa rinjayen suka dauka, wacce ta nuna cewa, saka tambaya kan asalin kasar da mutum ya fito, zai iya sa a hana mutum miliyan shida-da-dubu-dari-biyar, shiga kidayar, wadanda mafi akasarinsu Hispaniyawa ne.

Tuni dai manyan jami’an wasu jihohin Amurka, irinsu babbar Atoni Janar din birnin New York, Letitia James, suka fara kalubalantar batun saka tambayar a shirin kidayar, wanda za a yi a watan Afrilun badi.

To sai dai, daya daga cikin alkalan Kotun, Cif Justice John Roberts, ya ce, samun bayanai kan asalin kasar mutum, zai taimaka sosai wajen aiwatar dokar ‘yancin yin zabe a Amurka.

Facebook Forum

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG