Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabanin Fulani Da Na Hukumomin Tsaron Najeriya Sun Tattauna A Kebbi


Taron Shugabanin Fulani Da Hukumomin Tsaron Najeriya
Taron Shugabanin Fulani Da Hukumomin Tsaron Najeriya

A can baya, shugabannin kungiyoyin fulani a Najeriya sun sha kokawa akan rashin sauraren matsalolin fulani makiyaya da aka fi alakantawa da ayyukan ta’addanci musamman a arewacin kasar, abinda ake ganin na kara hura wutar tashe-tashen hankula a yankin.

Wannan ne ya sa a karon farko, wata kungiyar Fulani ta gudanar da wani babban taro a Birnin Kebbi, wanda ya hada hancin dukkan masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaron kasar, da kuma shugabannin fulani a dukkan matakai, a karkashin jagorancin Ministan Cikin Gidan Najeriya, Abdurrahman Dambazau.

Dambazau ya ce wannan taron wani bangare ne na matakan da ake dauka, domin samar da maslaha da kawo karshen rikici tsakanin fulani da manoma, kamar yadda ya ke kunshe a manufofin kasashen kungiyar rayar tattalin arzikin Afrika ta Yamma wato ECOWAS.

To sai dai Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Muhammed Adamu, yana ganin matsalolin tsaro da ake fama da su a arewacin Najeriya, sun wuce na fada tsakanin fulani da manoma.

Shima mai masaukin baki gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce shugaba Muhammada Buhari ne ya bada umarnin a hadu da duka shugabanin fulani na Najeriya, domin aji matsalolinsu da kuma samo hanyar da za a taimaka musu don inganta rayuwar su wajan samun zaman lafiyar kasar da bunkasar abinci.

A nasa bangaren shugaban kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah na kasa, Muhammadu Kirowa Ardo Zuru, yace tun da ake ba a taba dauko hanyar warware matsalar rikicin bafillace ba, duk abin da aka yi labari ne kawai da ake turo wasu, idan ma sun je ba za su fadi abinda ya ke gaskiyar magana ba.

Rahotanni sun nuna cewa taron na tsawon sa’o’i 3 da aka gudanar a sirrance ba tare da ‘yan jarida ba, ya kunshi fulani, ciki ko har da wadanda ake zargin suna cikin masu tada kayar baya, domin jin tasu bukatar da korafe-korafen, da zimmar warware kalu-balen tsaron yankin.

Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG