Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce a Gaggauta Tsagaita Wuta a Libiya


Janar Khalifa Haftar
Janar Khalifa Haftar

Yayin da bangarori ke ta barin wuta kan juna a kasar Libiya ta yadda farar hula ke fama, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangaren Janar Khalifa Haftar bangaren gwamnati da su kwance damara.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi wani “Kira na gaggawa” na bukatar tsagaita wuta a yankunan da ke bayan garin Tripoli don ta kwashe fararen hula da kuma wadanda su ka samu raunuka, yayin da sojojin da suke biyayya ga kwamandan sojojin kasar, Janaral Khalifa Hafta, su ka ci gaba da kutsawa da nufinsu na kwace babban birnin kasar.

Firai Ministan Libya da ke samun gogyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, Fayez Sarraj, ya kira matakin na Haftar da kokarin juyin mulki. Haftar da sojojinsa sun samu nasarar karbe bayan garin Tripoli, babban birnin kasar, amma Sarraj ya ce dakarun gwamantinsa a shirye su ke su tunkare su.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Libya, ya bukaci du ka bangarorin biyu da su ke yankin da su cimma yarjajjeniyar tsagaita wuta ta jinkai.

Kafafafen yada labarai na kasashen larabawa, sun nuna wasu hotunan bidiyo na sojojin Haftar su na shiga kofofin filin jirgin sama na Tripoli da ya ke rufe a yanzu, kafin su zagaye wajen ginin filin jirgin, a kusa da hanyar tashi da saukar da ta ke rufe yanzu. Babu wata alamar tirjiya a yayin kwace wurin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG