“Ku yi abinda ya kamata, ku kada kuri'ar amincewa," wasu daga sakonnin da alamomin da aka kafa jikin gidaje a fadin birnin al-Khahira ke dauke da su kenan. Babu wani bayyanannen adawa.
Irin tallata manufarsu da masu goyon bayan gwamanti su ka yi din na kiran da a yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulki don bai wa shugaban kasar Masar, Abdel Fattah el-Sissi, damar ci gaba da zama a ofishinsa har zuwa shekarar 2030.
Mutanan kasar Masar da su ke zaune a kasashen waje za su fara kada kuri’arsu a yau juma’a, kuma za a fara jefa kuri’a na kasa baki daya a gobe Asabar – kasa da sati daya bayan da ‘yan majalisa su ka amince da matakin.
Facebook Forum