Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Kara Saka Takunkumi Akan Wasu Kasashe Uku


Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkar tsaro, ya bayyana cewa kasashe uku na yankin Latin Amurka za su fuskanci karin wasu takunkumai.

A yau Laraba ake sa ran gwamnatin Amurka za ta sanar da karin sabbin takunkumi akan Venezuela da Cuba da Nicaragua, a wani mataki na kara kuntatawa kasashen.

Ita dai gwamnatin shugaba Trump ta himmatu ne wajen ganin an kawar da Nicolas Maduro daga Caracas, babban birnin kasar, da zimmar nada shugaban majalisar dokokin kasar Juan Guiado a matsayin shugaban kasa, yunkurin da tuni wasu kasashe sama da 50 suka amince da shi.

Gabanin wani jawabi da mai bai wa shugaba Trump shawara kan harkar tsaro, John Bolton zai yi a yau Laraba, wani babban jami’in gwamnatin Amurka, ya jaddada cewa, za su iya daukan kowanne irin mataki akan Venezuelan.

A cewar Bolton, burin Amurka shi ne a mika mulki cikin ruwan sanyi, yana mai cewa sun kudurin aniyyar ganin an yi sauyin gwamnati.

A wani yunkurin na ganin an saka hukumomin Venezuela a wani yanayi na takura, Amurkan har ila yau ta kara nuna matsin lamba ga kasar Cuba, wacce take taimakawa hukumomin Venezuela.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG