Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar: Shugaba Al-Sisi Yayi Nasara A Zaben Raba Gardama


Bayan da aka sanar da zaben raba gardamar da aka yi a Masar, yanzu haka mutanen kasar sun amince da a yi wa kundin tsarin mulkin kasar garanbawul da zai bai wa shugaban kasar dama zama akan karagar mulki har zuwa 2030.

Kusan kashi 90 cikin 100 na al’umar kasar Masar da suka kada kuri’a a zaben raba gardama kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul ko akasin haka, sun amince da a yi kwaskwarimar, wacce za ta bai wa shugaba Abdel Fatah Al-sisi damar mulkar kasar har zuwa shekarar 2030.

A jiya Talata, shugaban hukumar zaben kasar, Alkali Lasheen Ibrahim Soliman Lasheen, ya bayyana sakamakon zaben raba-gardamar, wanda aka kwashe kwanaki uku ana yi.

Jim kadan bayan ayyana sakamakon ne, shugaba Al Sisi, ya hau shafinsa na Twitter, ya mika godiyarsa ga al’umar kasar ta Masar, ya kwatanta su a matsayin “wadanda suka farga da irin kalubalan da ke gaban kasar.”

Sai dai ‘yan adawa, sun zargi gwamnatin Al Sisi da tursasawa mutane su zabe ta, sannan sun zargi gwamnatin, da raba kayayyakin abinci da bayar da motocin yin jigilar mutane zuwa rumfunan zabe.

A cewar ‘yan adawan, yin sauyi ga kundin tsarin mulkin kasar, zai tauye tagomashin burin da ya sa aka yi juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG