Kungiyar WANEP ta Jamhuriyar Nijar da hadin gwiwar wata kungiyar DRC ta kasar Denmark sun kaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a a game da mahimancin gudunmowar mata wajen samar da tsaro a yankin Sahel.
A wani abu mai kama da dabarar cizawa da hurawa a lokaci guda, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana niyyar ganawa da Iran a yayin da kuma Amurka ke kara kakaba ma ta takunkumi.
Bayan da mahaukaciyar guguwar nan mai hade da ruwa da iska da aka yiwa lakabi da "Dorian" ta lalata tsibirin Bahamas, yanzu haka ana neman taimakan gaggawa ga mutanan tsibirin.
Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga 'yan kasarta da kada su kai harin ramuwar gayya ga kamfanonin kasar Afurka Ta Kudu da ke kasar.
Kungiyar ta yi Allah wadai da kashe 'yan Najeriya a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, kafin daga bisani ta yi musu karin bayanin matsayinta akan wannan abu da yaki ci yaki cin yewa na abka wa 'yan Najeriya a kasar Afurka Ta Kudu.
Sakamakon farko na binciken da wakiliyar Majalisa Dinkin Duniya, Agnes Callamard, ta yi, ya yi kira akan a gaggauta kawo karshen ta'addanci a Najeriya.
Jihar Zamfara ta zama ta farko a duk fadin Najeriya wajen fara kaddamar da shirin Ruga da za a tsugunar da Fulani makiyaya da ma sauran al'umma masu yin kiwo a duk fadin jahar.
Mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da "Dorian" da ba'a taba ganin irinta ba a cikin shekaru 84, ta doshi wasu jihohi a Amurka.
Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da kuma kare hakkin dan Adam irin su SERAP da EiE da kuma wasu ‘yan kishin kasa su 6,721 sun amince a shigar da kara kan yadda ‘yan majalisar dokoki a Najeriya za su kashe kudi har Naira biliyan 5 da rabi wajen sayen motocin kawa.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka wato FBI ta ce dan bindigar nan da ya kashe mutane bakwai ya kuma raunata mutane 22 a garin Odessa a ranar Asabar, shi kadai ya aikata kuma ta yuwu bashi da alaka da wata kungiyar ‘yan ta’adda ta gida ko ta waje.
Amurka da China sun sa sabbin haraji kan kayakin juna na saidawa kasashen a jiya Lahadi, wannan fafatawa ta baya-bayan nan wani bangare ne na dadadden yakin cinakayyar da ake yi tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.
Firaiministan Bahamas, Hubert Minnis, ya bayyana jiya Lahadi da, a ta bakinsa, “rana mafi muni a rayuwata” yayin da mahaukaciyar guguwar nan da aka yi wa lakabi da Hurricane Dorian ta abkawa tsibirin da ake ganin ita ce guguwa mafi karfi da ta bullo a yankin na Atlantika cikin shekaru 84.
Wannan karin da Amurka ta yi yana zuwa ne bayan da gwamantin kasar ta nemi gwamnatin Najeriya da ta duba karin kudin izinin shiga kasarta, wato biza, da ta kara wa Amurkawa, inda ta nemi a rage shi.
Domin Kari