Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce bukatar yaki da ‘yan fasakwabri ta sanya shi ba da umurnin rufe kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Shugaban na magana ne a taron raya tattalin arzikin Afirka a Japan, yayin da ya ke ganawa da shugaban Benin, Patrice Tallon, da ke cewa rufewar na kawo koma baya ga kasarsa.
Shugaba Buhari ya ce illar ‘yan sumoga musamman kan shigo da shinkafa na kawo nakasu ga aikin noman shinkafa a cikin gida, amma duk da haka ya ce zai duba yiwuwar bude iyakar nan gaba kadan bayan ganawa da shugaban na Benin da na Jamhuriyar Nijar, Muhammad Issoufou.
Tun farkon gwamnatin Buhari ya ba da umurnin rufe kan iyaka ta kasar musamman don hana shigo da shinkafa da zummar raya noman shinkafar a gida.
Shugaban Hukumar Hana Fasakwabri, Hamid Ali, ya ce dalilan ma har da na rashin kayan aikin gwada ingancin shinkafar.
Masanin tattalin arziki Yushau Aliyu na da ra’ayin rashin ribar rufe iyakar ya fi ribar yawa.
Yanzu dai a kasuwannin Najeriyar akwai shinkafar da ake sarrafawa cikin gida rufe a buhuna masu sheki duk da ba lallai ne shinkafar na da marmari a abinci ba, ko farashi mai matukar rangwame.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum